Gwamna Abubakar Bello na jihar Neja ya zabi Ahmed Garba matsayin Sabon sarkin Kagara

Gwamna Abubakar Bello na jihar Neja ya zabi Ahmed Garba matsayin Sabon sarkin Kagara

- Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya amince da naɗin Ahmed Garba Gunna a matsayin sabon sarkin Kagara

- An naɗa sabon sarkin ne biyo bayan rasuwar sarkin Kagara Alhaji Salihu Tanko, wanda ya rasu ranar 2 ga watan Maris ɗin da ya gabata

- Gwamna Bello ya taya sabon sarkin murna kuma ya bayyana shi da cewa ya yi matuƙar da cewa da karagar Mulkin a yanzun

Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya taya sabon sarkin kagara, Ahmed Garba Gunna murnar zama sarki a masarautar ta Kagara.

An naɗa Garba Gunna a matsayin sabon sarkin ne biyo bayan rasuwar sarki Alhaji Salihu Tanko, wanda ya rasu ranar 2 ga watan Maris 2021 bayan shafe shekaru 39 a kan karagar mulki.

KARANTA ANAN: Hotunan ɓarawon da aka kama yana sharɓar barci a gidan ɗan sandan da ya shiga yi wa sata

Ahmed Gunna ya samu ƙuri'u mafi rinjaye a zaɓen da yan majalisar zaɓen sarki na masarautar Kagara suka gudanar, kuma hakan ya bashi nasarar zama sarkin.

A wani jawabi da gwamnan ya fitar, ya bayyana Ahmed da cewa ya yi matuƙar dacewa da zama sarkin, ya ƙara da cewa zaɓen da yan majalisar masarautar suka masa ya nuna cancantar sa na riƙe masarautar.

Gwamnan ya ce, a matsayinsa na ƙwararren ma'aikaci, sabon sarkin yana da kwarewar da zai gina masarautar daga inda aka barta ta hanyar rike al'adunta.

Gwamna Abubakar Bello na jihar Neja ya taya Sabon sarkin Kagara Murna
Gwamna Abubakar Bello na jihar Neja ya taya Sabon sarkin Kagara Murna Hoto: Chief Press Scretary FB post
Asali: Facebook

A cewar gwamnan, wanda sakataren yaɗa labaransa ya saka a shafinsa na Facebook, ya ce:

"Zaben da aka yi ma sabon sarkin bayan ya rike muƙamin ɗan majen kagara a masarautar, ya nuna yarda da imanin da mutanen masarautar ke dashi akansa wajen kawo cigaba da riƙe al'adun mutane."

Gwamnan ya ƙara da tuna ma sabon sarkin cewa, zai amshi karagar mulki a wani yanayi da ake ciki na rashin tsaro.

KARANTA ANAN: Tsohon Shugaban kasa Jonathan ya bayyana babban abin da yake kashe Najeriya a yau

Gwamnan ya roƙi sabon sarkin da ya yi amfani da kwarewar da yake da ita wajen haɗa kai da masu ruwa da tsaki don kawo dawwamammen zaman lafiya a yankin.

Sannan gwamnan ya yi kira ga mutanen dake ƙarƙashin masarautar Kagara da su nuna goyon bayan su ga sabon sarkin wajen dawo da zaman lafiya, jituwa a tsakaninsu, don kawo cigaba a yankin dama jihar baki ɗaya.

Kafin naɗin sabon sarkin, ya kasance shugaban riƙo na hukumar tara haraji na jihar Neja kuma shine Ɗan majen Kagara.

A wani labarin kuma Mutum 8 sun hallaka, da dama sun jikkata a wani sabon harin yan bindiga a jihar Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta bayyana cewa an kashe mutane 8, kuma an jikkata mutum huɗu a wasu hare-hare da suka kai a Kajuru da Kachia.

Kwamishinan yaɗa labarai da kuma harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: