Yusuf Buhari zai auri 'yar Sarkin Bichi, Nasir Ado Bayero

Yusuf Buhari zai auri 'yar Sarkin Bichi, Nasir Ado Bayero

- Ba da dadewa ba, dan shugaban kasan Najeriya zai angwance

- A cewar majiya, Yusuf Buhari zai auri 'yar gidan Sarkin Bichi

- Wannan shi ne aure na uku da Buhari zai yiwa 'yayansa tun da ya hau mulki

Yusuf Buhari, dan gidan shugaban kasa Muhammadu, na shirin angwancewa da diyar Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero, Zahra Ado Bayero, rahoton Daily Nigerian.

Zahra Bayero yanzu haka na karatun ilmin zanen gine-gine a kasar Birtaniya yayinda shi Yusuf Buhari ya kammala karatunsa a jami'ar Surrey, Guildford, a Birtaniya.

Majiyoyi sun bayyana cewa za'a gudanar da bikin cikin watanni biyu zuwa uku.

"An kaddamar da shirye-shiryen bikin. Kamar yadda al'ada ta tanada, iyayen mijin sun kai gaisuwa wajen iyayen Zahra," cewar majiyar da aka sakaye sunanta.

Majiyar ta kara da cewa da tuni an yi bikin amma saboda rashin kasancewar mahaifiyar Yusuf, hajiya Aisha Buhari, wacce ta dawo daga Dubai inda ta kwashe watanni shida.

"Tun da yanzu ta dawo ana gab da azumi, lallai za'a yi daurin auren bayan Sallah," majiyar ta kara.

DUBA NAN: Majalisar Dattijai ta amince da wani Naɗin da Buhari ya turo mata na wani Babban Muƙami

Yusuf Buhari zai auri 'yar Sarkin Bichi, Nasir Ado Bayero
Yusuf Buhari zai auri 'yar Sarkin Bichi, Nasir Ado Bayero
Asali: UGC

KU KARANTA: JAMB ta bayyana Ranar da zata fara saida Fom ɗin Zana Jarabawar UTME 2021

Kun ji cewa uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta dawo gida Najeriya bayan watanni shida a birnin Dubai, kasar haddadiyar daular Larabawa.

Legit Hausa ta samu labari daga majiya mai karfi cewa Aisha tana fadar shugaban kasa da ranan nan.

Uwargidar shugaban kasan ta tafi Dubai ne tun bayan auren diyarta, Hanan, a Satumban 2021.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel