JAMB ta bayyana Ranar da zata fara saida Fom ɗin Zana Jarabawar UTME 2021

JAMB ta bayyana Ranar da zata fara saida Fom ɗin Zana Jarabawar UTME 2021

- Hukumar JAMB ta fitar da jadawalin saida fom din zana jarabawar shiga gaba da sakandire UTME na wannan shekarar 2021

- JAMB ta sake jaddada cewa duk wani dalibi da ke son zana jarabawar to ya zama wajibi ya mallaki lambar katin zama dan kasa wato NIN

- Ta Bayyana za'a fara siyar da fom din ranar takwas ga watan Aprilun wannan shekarar da muke ciki.

Hukumar dake da alhakin shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire JAMB ta fitar da jadawalin yadda jarabawar share fagen shiga jami'a UTME na bana zai kasance.

KARANTA ANAN: Majalisar Dattijai ta amince da wani Naɗin da Buhari ya turo mata na wani Babban Muƙami

Kamar yadda hukumar JAMB ta fitar, za'a yi jarabawar UTME daga ranar Asabar 5 ga watan Yuni zuwa Asabar 19 ga watan na Yuni.

Hukumar ta kuma bayyana cewa za'a fara rijistar neman izinin zana jarabawar ta bana daga ranar Alhamis takwas ga watan Afirilu zuwa ranar Asabar 15 ga watan Mayu.

Haka zalika, hukumar JAMB ta ce babu wani ƙarin lokaci da zata yi na siyar da fom din UTME ko kuma na DE.

Hukumar ta fitar da wannan sanarwar ta hannun shugabanta dake kula da bangaren yaɗa labarai, Dr Fabian Benjamin, a yau Laraba.

Sanarwar ta bayyana cewa dole ɗuk wani ɗalibi ya tanaji lambar katin zama ɗan kasa wato NIN kafin ya yi rijista, jaridar The Nation ta ruwaito.

JAMB ta bayyana Ranar da zata fara saida Fom ɗin Zana Jarabawar UTME 2021
JAMB ta bayyana Ranar da zata fara saida Fom ɗin Zana Jarabawar UTME 2021 Hoto: thenationonlineng.net
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Na shirya: Budurwa ta tsayar da ranar da za a daura aurenta ba tare da miji ba, ta buga katin gayyata

JAMB ta ƙara da cewa amfani da lambar katin zama ɗan ƙasa NIN wajibi ne ga duk wanda keson zana jarabawar bana 2021.

Ta kuma bayyana cewa za'a yi rijistar jarabawar a cibiyoyin zana jarabawar 700 dake faɗin ƙasar nan.

A wani labarin kuma Taƙaddama ta ɓarke a Majalisar Dattijan Ƙasar nan kan cewa Wata ƙaramar Hukuma a Arewa ta zarce Jihar Bayelsa

Taƙaddamar ta fara ne daga lokacin da Sanata daga jihar Adamawa, Aishatu Binani ta kawo misalin cewa ƙaramar hukumar Mubi ta zarce jihar Bayelsa girma.

Sai dai misalin be ma Sanata Dickson daga jihar Bayelsa daɗi ba inda ya mike ya gargaɗe ta da tayi abinda ke gabanta ta daina saka jihar sa a ciki.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban- daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: