Majalisar Dattijai ta amince da wani Naɗin da Buhari ya turo mata na wani Babban Muƙami

Majalisar Dattijai ta amince da wani Naɗin da Buhari ya turo mata na wani Babban Muƙami

- Majalisar dattijai ta amince da bukatar shugaba Muhammadu Buhari na nadin shugaban hukumar dake kula da gidan gyaran hali wato kurkuku

- Majalisar ta amince da nadin ne biyo bayan sauraron rahoton da kwamitin ta ya bayyana a zaman ta na yau Laraba

- Shugaban Kwamitin sanata Kashim Shettima na jam'iyyar APC ne ya bayyana rahoton inda yace Nababa ya cancanci ya rike ofis din

A ranar Laraban nan majalisar dattijai ta amince da naɗin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya turo mata na shugaban hukumar gyaran hali masu kula da kurkuku.

Majalisar ta amince da Haliru Nababa a matsayin shugaban hukumar gyara hali wato (Correctional Service).

KARANTA ANAN: Kotu ta bada umarnin tsawaita wa'adin rajistar NIN zuwa watanni biyu

Amincewa da naɗin ya biyo bayan dubawa da kuma yarda da rahoton da kwamitin kula da ayyukan cikin gida na majalisar ya gabatar, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Lokacin da yake gabatar da rahoton, shugaban kwamitin, Sanata Kashin Shetima, na jam'iyyar APC daga jihar Borno yace babu wani rahoto na ƙara ko wani laifi da wanda akeson naɗawa yayi.

Ya kuma ƙara da cewa Haliru Nababa ya nuna matuƙar ƙwarewa da bayyana ya cancanta da ya riƙe wannan ofis ɗin.

Shetima yace Nababa ya cika sharuɗɗan sashi na 3 (2) na kundin tsarin hukumar gyaran hali ta ƙasar nan.

Majalisar Dattijai ta amince da wani Naɗin da Buhari ya turo mata na wani Babban Muƙami
Majalisar Dattijai ta amince da wani Naɗin da Buhari ya turo mata na wani Babban Muƙami Hoto: @NGRsenate
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Ahmad Lawan: Ba tsige Buhari ne zai kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya ba

Shugaban kwamitin ya ƙara da cewa:

"Wanda ake son naɗawa ya bayyana a gaban kwamitin mu domin tantancewa, ya kuma bayyana cewa rashin isassun makamai domin hana karya magarƙama, rashin isassun kuɗi, rashin yin kasafi me kyau a hukumar, da kuma rashin tsaruka masu kyau a hukumar sune manyan kalubalen da suka dabai-baye hukumar."

Shettima ya ƙara da cewa: "Nababa ya kuma bayyana cewa cinkoson masu laifi a kurkuku na daga cikin abinda zai tasa a gaba idan ya shiga ofis, yace zai iya bakin kokarin sa wajen samar da wurare a kurkukun ƙasar nan, zamu haɗa hannu da masu ruwa da tsaki da gwamnoni wajen cimma manufar mu."

A wani labarin kuma Gwamnatin Buhari ta ware zunzurutun kudi N1.13bn don gina hanyoyi 12

Gwamnatin ta bayyana aikin da cewa, dukkan jihohin kasar za su ci gajiyarsa ciki har da FCT.

Ministan Ayyuka da Gidaje ya bayyana ana bukatar karin wasu kudaden don cimma burin.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77.

Asali: Legit.ng

Online view pixel