NDLEA: Marwa yayi kira ga fara yiwa 'yan siyasa da dalibai gwajin shan kwayoyi
- Shugaban NDLEA ya yi kira ga yiwa 'yan siyasa da dalibai gwajin shan miyagun kwayoyi
- Shugaban ya kuma bayyana yadda adadin shan miyagun kwayoyi ke hau-hauwa a Najeriya
- Ya bayyana cewa, hakan zai taimaka wajen samar da mulki mai inganci a fadin kasar Najeriya
Birgediya-Janar Buba Marwa ya yi kira da a gudanar da gwajin shan kwayoyi ga dalibai da ‘yan siyasa, musamman wadanda ke takarar ofisoshin gwamnati a kasar, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Marwa, wanda shi ne Shugaba kuma Babban Darakta na Hukumar hana Sha da fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA), ya yi wannan kiran ne a ranar Laraba a wata ganawa da Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, a Marina.
KU KARANTA: 'Yan sanda sun sheke 'yan bindiga, sun kwato bindigogi da mota a Kaduna
An ruwaito shi yana fada a cikin wata sanarwa daga Babban Sakataren yada labarai na gwamnan, Gboyega Akosile cewa:
“Neman ofisoshin gwamnati babban aiki ne. Bai kamata ku kasance cikin wannan muhimmin aiki na jama'a ba sannan kawunanku na cike saboda shaye-shaye,"
Ya kara da cewa,
“Matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi yanzu annoba ce a Najeriya. Yaduwarta ya kai kashi 15; sau uku na matsakaita a duniya. Daya cikin bakwai na ‘yan Najeriya na shan kwayoyi. Mun gano cewa akwai alaka tsakanin amfani da kwayoyi da aikata laifi.”
Ya yaba wa kokarin da gwamnatin jihar ta yi a kan batun shaye-shayen miyagun kwayoyi a cikin Jihar, yana mai bayyana Lagos a matsayin jiha ta farko a Najeriya da ta sanya wasu hanyoyi na zamani don yakar matsalar.
Dangane da wannan, Marwa ya nemi gwamnati da ta jagoranta tare da gudanar da gwajin shan kwayoyi ga dalibai a cikin jihar.
A cewarsa, abinda ya shafi shaye-shayen miyagun kwayoyi ya fi shafar matasa, wanda hakan ya zama dole ga dalibai, musamman wadanda ke manyan makarantu su yi gwajin na shan kwayoyi.
KU KARANTA: Matsalarmu ba shugabancin 2023 bane, adalci muke so a yiwa mutane, Makinde
A wani labarin daban, Gwamnatin jihar Kano ta haramta sayar da sinadarin dan tsami da danginsa a fadin jihar baki daya, biyo bayan wata cuta da ake zargin sinadarin ya haifar ga jama'a.
Shugaban hukumar kare hakkin masu sayan kayayyaki Baffa Babba Dan Agundi ne ya bayyana hakan a hirar da ya yi da BBC.
Baffa ya ce bincike ya nuna cewa wadannan sinadaran da ake hada kayan shaye-shaye da su da yawansu lokacin ingancinsu ya kare, don haka babu mamaki dan an ce suna cutar da masu amfani da su.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng