2023: Ba zan goyi bayan Jonathan ba idan ya tsaya takara a APC, in ji Wike

2023: Ba zan goyi bayan Jonathan ba idan ya tsaya takara a APC, in ji Wike

- Nyesom Wike, ya ce ba zai goyi bayan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba idan ya fito takara a jam'iyyar APC mai mulki

- Wike ya ce shi mutum ne mai kishin jam'iyyarsa ta PDP don haka ba zai ci amanarta ba

- Sai dai kuma ya sha alwashin marawa tsohon shugaban kasar baya idan ya samu tikitinsa a karkashin jam'iyyarsa

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce ba zai goyi bayan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba ko da ya samu tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben 2023.

Da yake magana da sashin BBC Pidgin a karshen mako a Fatakwal, gwamnan ya kuma ce Allah ya yi amfani da shi wajen zamar da Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, gwamnan Ribas.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An yi barin wuta yayinda yan bindiga suka far ma ayarin motocin wani gwamna

2023: Ba zan goyi bayan Jonathan ba idan ya tsaya takara a APC, in ji Wike
2023: Ba zan goyi bayan Jonathan ba idan ya tsaya takara a APC, in ji Wike Hoto: @GovWike
Asali: Twitter

Wike ya ce shi kansa Jonathan ya san cewa shi (Wike) ba zai yi aiki tare da shi ba idan ya koma APC sannan ya samu tikitin jam’iyyar don tsayawa takarar Shugaban kasa a 2023.

Ya ce: “Ni dan PDP ne, idan tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nemi tikitin tsayawa takara a jam’iyyata, zan mara masa baya. Ba zan iya cin dunduniyar jam’iyya ba. Amma idan ya nemi tikitin tsayawa takara a APC, ba zan goya masa baya ba saboda ba zan iya nuna adawa da jam’iyyata ba.

“Ya san ba zan mara masa baya a APC ba koda kuwa daga kudu ya fito. Ba na yin irin wannan siyasar. Muna magana ne a kan jam’iyya kuma bana wasa da kabilanci.”

Wike ya yi wa Amaechi ba'a saboda ya kira shi a matsayin ma'aikacin sa yana mai cewa Ministan Sufuri ba zai mulki jihar ba idan da Allah bai yi amfani da shi wajen nada shi gwamna ba a wancan lokacin.

Ya ce Amaechi ya manta lokacin da ya fada a coci cewa bayan Allah a rayuwarsa, mutum na biyu shi (Wike) yana mai kara da cewa ya kasance da ‘yancin zabar kowane irin mukami a gwamnatin Amaechi saboda irin gudummawar da ya bayar.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga: Idan zinare suke so, toh su nema mana sannan su bar mutanena su sarara, Sarkin Birnin Gwari

A wani labarin, Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike bai da niyyar barin jam’iyyar siyasarsa ta yanzu, wato jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Gwamna Wike ya shaida wa BBC Pidgin a wata hira da ya yi cewa lalacewar da ke cikin APC ya fi matsalolin da PDP ke fuskanta a halin yanzu.

Yayin da ya kwatanta matsalolin da jam'iyyarsa ke fuskanta a yanzu da zazzabin cizon sauro, ya bayyana matsalolin cikin gida na APC a matsayin cutar kansa mai tsanani.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng