APC tana da cutar Kansa, ba zan taba sauya sheka zuwa jam'iyyar ba, Wike ya bayyana

APC tana da cutar Kansa, ba zan taba sauya sheka zuwa jam'iyyar ba, Wike ya bayyana

- Gwamnan PDP a jihar Ribas, Nyesom Wike ya musanta cewa yana shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki

- Gwamna Wike yayi zargin cewa APC ta rube sosai kamar yadda take a mataki na hudu na cutar kansa wanda ba a iya warkarwa

- Lauyan da ya zama dan siyasa ya ce ya gwammace ya zauna a PDP tare da matsalolin ta maimakon sauya sheka zuwa APC da manyan matsalolin ta

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike bai da niyyar barin jam’iyyar siyasarsa ta yanzu, wato jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Gwamna Wike ya shaida wa BBC Pidgin a wata hira da ya yi cewa lalacewar da ke cikin APC ya fi matsalolin da PDP ke fuskanta a halin yanzu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An yi barin wuta yayinda yan bindiga suka far ma ayarin motocin wani gwamna

APC tana da cutar Kansa, ba zan taba sauya sheka zuwa jam'iyyar ba, Wike ya bayyana
APC tana da cutar Kansa, ba zan taba sauya sheka zuwa jam'iyyar ba, Wike ya bayyana Hoto: @GovWike
Source: Twitter

Yayin da ya kwatanta matsalolin da jam'iyyarsa ke fuskanta a yanzu da zazzabin cizon sauro, ya bayyana matsalolin cikin gida na APC a matsayin cutar kansa mai tsanani.

Ya ce:

"Idan na kamu da cutar zazzabin cizon sauro, shin zan je neman cutar kansa? A lokacin da na kamu da cutar zazzabin cizon sauro mai sauƙin magancewa, kuna so na bi kansar da za ta kashe ni nan take. Wace jam’iyya? APC da ta kashe Najeriya?

"Wace jam'iya zan je. Duk wani fadan da ya taso a PDP, zan tsaya a can in tuttura shi. Idan na ji rauni, babu komai. Idan na yi musu rauni, shima haka. Amma babu inda zan gudu in je. Bayan haka, na san cewa ba za su iya yi min rauni ba.

"Amma barin PDP wacce ke da Malaria zuwa APC wacce ke da cutar kansa mataki na hudu, ah!"

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga: Idan zinare suke so, toh su nema mana sannan su bar mutanena su sarara, Sarkin Birnin Gwari

A wani labarin, Dino Melaye, tsohon sanatan da ya wakilci jihar Kogi ta yamma, yace babbar damfarar da ta taba faruwa a Afrika shine yadda aka goyawa Buhari baya ya samu shugabancin kasa a 2015.

Melaye ya sanar da hakan ne a ranar Juma'a yayin da ya bayyana a wani shiri na gidan talabijin na Channels.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, Melaye, wanda yanzu dan babbar jam'iyyar adawa ce ta PDP, ya bar jam'iyyar APC a shekarar 2018.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit.ng

Online view pixel