Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun sake kai hari Kaduna, sun kashe uba da ‘da

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun sake kai hari Kaduna, sun kashe uba da ‘da

- Jihar Kaduna ta sake fadawa halin alhini yayinda yan bindiga suka kai sabon hari kauyen Baka, karamar hukumar Igabi da ke jihar

- 'Yan fashin sun harbe wani uba da dan shi har lahira saboda bijirewa yunkurin sace su

- Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida na Kaduna ya tabbatar da harin wanda ya faru a ranar Asabar, 13 ga watan Fabrairu

Wasu da ake zargin ‘yan fashi ne sun kai sabon hari kauyen Baka, karamar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna, inda suka kashe uba da dansa a safiyar ranar Asabar, 13 ga watan Fabrairu.

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, ya tabbatar da ci gaban, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Gwamnonin Nigeria 2 sun kara albashin ma’aikata duk da matsin tattalin arziki

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun sake kai hari Kaduna, sun kashe uba da ‘da
Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun sake kai hari Kaduna, sun kashe uba da ‘da Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

Kwamishinan ya ce 'yan fashin sun yi ta harbi ba kakkautawa sannan suka shiga gidan mamacin wanda ya kasance manomi a yankin ta karfin tuwo.

Sun yi yunkurin garkuwa da shi da ɗansa sannan kuma a karshe suka harbe su sakamakon turjiyar da suka nuna masu.

Kwamishinan ya ce Gwamna Nasir El-Rufai ya nuna bakin ciki kan harin sannan ya jajantawa dangin wadanda harin ya rutsa da su. Ya kuma yi wa mamatan addu'o'in samun jin kai.

KU KARANTA KUMA: Rijista: Dino Melaye ya caccaki mambobin APC kan shirin sabonta rijistar jam’iyyar

A gefe guda, Gwamnan jihar Kano, Abdullahu Umar Ganduje, ya yi zargin cewa takwararsa na jihar Kano, Malam Nasir El-Rufa'i, bai fahimci matsalar tsaron da Arewa ko fuskanta ba ko kuma ba'a fahimceshi ba.

El-Rufa'i ya yi jawabi a hirarsa da BBC cewa babu hadin kai tsakanin gwamnonin Arewa wajen yakan matsalan tsaro.

Amma Ganduje a hirarsa da Rediyan Faransa ranar Alhamis, ya bayyana cewa ya taba magana da El-Rufa'i da gwamnan Bauchi kan yadda za'a magance matsalar.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel