Ina ganin El-Rufa'i bai fahimci matsalar rashin tsaro ba, Ganduje

Ina ganin El-Rufa'i bai fahimci matsalar rashin tsaro ba, Ganduje

- Gwamnan Ganduje na Kano ya ce shi da kansa ya shirya taron tattaunawa kan tsaro da El-Rufa'i

- A cewar Ganduje, bai fahimci dalilin da yasa gwamnan yace babu hadin kai tsakaninsu ba

- Ko wace jiha na da nata salon magance matsalar da kuma irin abinda take fuskanta

Gwamnan jihar Kano, Abdullahu Umar Ganduje, ya yi zargin cewa takwararsa na jihar Kano, Malam Nasir El-Rufa'i, bai fahimci matsalar tsaron da Arewa ko fuskanta ba ko kuma ba'a fahimceshi ba.

El-Rufa'i ya yi jawabi a hirarsa da BBC cewa babu hadin kai tsakanin gwamnonin Arewa wajen yakan matsalan tsaro.

Amma Ganduje a hirarsa da Rediyan Faransa ranar Alhamis, ya bayyana cewa ya taba magana da El-Rufa'i da gwamnan Bauchi kan yadda za'a magance matsalar.

Ya ce shi ya janyo hankulansu bisa shawaran da jami'an tsaro suka bada kan yadda sauran jihohi yankin zasu amfana da dajin Falgore dake jihar Kano.

Ganduje ya ce gwamnatin Bauchi da Kaduna sun turo wakilansu wajen ganawa kan matsalar tsaro kuma sun tattauna da mafiya, shiyasa jawabin El-Rufa'i ke bashi mamaki.

KU DUBA: 'Yan sanda: Shanun da suka kutsa gidan Soyinka na wani bayerabe ne ba bafulatani ba

Ina ganin El-Rufa'i bai fahimci matsalar rashin tsaro ba, Ganduje
Ina ganin El-Rufa'i bai fahimci matsalar rashin tsaro ba, Ganduje Credit: Ganduje TV
Asali: UGC

KU KARANTA: Rashin tsaro: A haramtawa makiyayan kasashen ketare shigowa kasar nan, Ganduje

"Da farko, maganar rashin hadin kai. Ban san dalilin fadin haka ba. Jami'an tsaro sun bamu shawaran cewa Kano, Kaduna da Bauchi su turo wakilansu Kano domin tattaunawa kan magance matsalar dajin Falgore da kuma yadda tsagerun yan bindiga ke amfani da dajin," Ganduje yace.

"Na yi magana da gwamnan Kaduna da Bauchi kuma suka turo wakilai inda kowa ya bada gudunmuwar duniya kuma akayi aikin kuma aka samu nasara. Ban fahimci maganar rashin hadin kai ba."

"A nawa tunain, shi (El-Rufa'i) bai fahimci matsalar sosai ba. Saboda kowani matsalar tsaro ya danganta da sababi. Duk irin hadin kan da mukayi, dole salonmu ya banbanta."

Kun ji cewa Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi magana game da matsalar da jihohin Arewa maso yamma su ke fuskanta na miyagun ‘yan bindiga.

Mai girma Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya zanta da jaridar BBC Hausa, inda ya shaida cewa babu hadin-kai tsakanin jihohin yankin.

Malam Nasir El-Rufai ya ce akwai fahimta tsakaninsa da takwaransa na jihar Neja, amma a cewarsa, ba haka abin yake da sauran gwamnoni ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel