Gwamnonin Nigeria 2 sun kara albashin ma’aikata duk da matsin tattalin arziki
- An sanar da ma’aikata a jihohin Ribas da Imo game da sabbin manufofi kan biyan albashi
- An aiwatar da manufofin ne do bin dokar gwamnatin tarayya kan sabon mafi karancin albashi
- Duk da haka, gwamnatin jihar Imo ta ce ma’aikatanta za su samu fiye da yawan albashin da gwamnatin tarayya ta amince da shi
An kara albashin ma’aikatan gwamnati a jihohin Ribas da Imo bisa daidai da tsarin biyan karancin albashi na N30,000.
Gwamna Nyesom Wike na Ribas da takwaransa na Imo, Hope Uzodinma, sun sanar da cewa daga yanzu ma’aikata a jihohin su za su ci moriyar sabon mafi karancin albashin tare da gyara a albashin kowa kamar yadda gwamnatin tarayya ta amince.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan sanda sun kama masu zanga-zanga da dama a Lekki tollgate
Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa gwamnatin jihar Ribas ta sanar da aiwatar da manufar a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, 11 ga watan Fabrairu, ta hannun kwamishinan yada labarai da sadarwa, Paulinus Nsirim.
Sanarwar ta ce:
“Mai girma, Nyesom Wike, cikin karimci ya amince da biyan mafi karancin albashi na N30,000 a kowane wata ga ma'aikatan Ma’aikatan Jihar Ribas tare da irin wannan gyara na albashi kamar yadda Gwamnatin Tarayya ta amince da shi.”
Gwamnatin Imo ta yi irin wannan sanarwar a ranar Juma’a, 12 ga Fabrairu, ta hannun kwamishinan labarai na jihar, jaridar The Nation ta ruwaito.
Emelumba ya bayyana cewa Gwamna Hope Uzodimma ya ba da umarnin biyan ma’aikacin da ke karbar mafi karancin albashin gwamnatin jihar N32,000 duk wata.
KU KARANTA KUMA: Babbar magana: An kama ango yana tarawa da kawar amarya a ranar daurin aurensu
A wani labari na daban, Kungiyar Gwamnonin Najeriya a ranar Alhamis ta yi ittafaki kan "bukatar samar da sabbin hanyoyin kiwon shanu domin maye gurbin kiwo a fili, da dare da kuma kiwon shanun da kananan yara ke yi a fadin tarayya."
A takardar da kungiyar ta saki bayan zamanta na 25 kuma shugabanta, gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya rattafa hannu, gwamnonin sun yi shawaran "samar da hanyoyin aiwatar da shirin da kwamitin sauya salon kiwo a fadin tarayya ta kawo."
Gwamnonin sun yi ittifakin magance matsalar rashin tsaro wanda ke da nasaba da Makiyaya masu aikata na'ukan laifuka daban-daban, Channel TV ta ruwaito.
Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.
Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.
Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.
Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411
Asali: Legit.ng