Rijista: Dino Melaye ya caccaki mambobin APC kan shirin sabonta rijistar jam’iyyar

Rijista: Dino Melaye ya caccaki mambobin APC kan shirin sabonta rijistar jam’iyyar

- Wasu yan Najeriya sun cika da mamaki da adadin magoya bayan APC da suka sabunta rijistarsu

- Daya daga cikin wadanda suka cika da al’ajabi kan haka shine Dino Melaye, tsohon sanata daga Kogi

- Melaye ya bayyana a ranar Asabar, 13 ga watan Fabrairu, cewa wadanda ke muradin shiga tsarin a daidai lokacin da ake tsaka da tsadar rayuwa suna da gagaruman matsaloli

Tsohon sanata daga jihar Kogi, Dino Melaye, ya caccaki mambobin jam’iyyar All progressives Congress (APC) da ke tururuwar fitowa a fadin Najeriya don sabonta rijistarsu na ‘ya’yan jam’iyyar.

A shafinsa na Twitter a ranar Asabar, 13 ga watan Fabrairu, tsohon dan majalisar ya jero wasu lamuran da ke addabar kasar a karkashin gwamnatin APC.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya nada wani sabon shugaban tsaro

Rijista: Dino Melaye ya caccaki mambobin APC kan shirin sabonta rijistar jam’iyyar
Rijista: Dino Melaye ya caccaki mambobin APC kan shirin sabonta rijistar jam’iyyar Hoto: dino_melaye
Asali: Twitter

Melaye ya ambaci karin farashin shinkafa, man fetur, sufuri (har na sama) a matsayin wasu daga cikin matsalolin da yan kasar suka tsinci kansu a ciki.

Ya kara da cewa idan har a tsaka da wadannan yanayi mutane da dama na so a kirasu da yayan jam'iyyar mai mulki , toh suna da manyan matsaloli.

Martaninsa:

"Kuna siyan buhun shinkafa akan N30,000 da mai a kan N170 kowace lita yanzu zai koma N200 a kowace lita, tikitin tattalin arziki zuwa lagos akan N60. Amma duk da haka kuna shirin sabonta rijistar ku na APC.

”Mutanena, matsalarku babba ce.”

A wani labarin, mun ji cewa an kara albashin ma’aikatan gwamnati a jihohin Ribas da Imo bisa daidai da tsarin biyan karancin albashi na N30,000.

Gwamna Nyesom Wike na Ribas da takwaransa na Imo, Hope Uzodinma, sun sanar da cewa daga yanzu ma’aikata a jihohin su za su ci moriyar sabon mafi karancin albashin tare da gyara a albashin kowa kamar yadda gwamnatin tarayya ta amince.

KU KARANTA KUMA: FG ta ce ma’aikatan jami’a sun yarda da janye yajin aiki, ta yi karin haske kan bude jami’o’i a fadin kasar

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa gwamnatin jihar Ribas ta sanar da aiwatar da manufar a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, 11 ga watan Fabrairu, ta hannun kwamishinan yada labarai da sadarwa, Paulinus Nsirim.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng