Cryptocurrency: ‘Dan Osinbajo ya rubutawa CBN takarda, ya soki matakin da aka dauka

Cryptocurrency: ‘Dan Osinbajo ya rubutawa CBN takarda, ya soki matakin da aka dauka

- Fiyin Osinbajo ya bayyana irin moriyar da ake ciki da tsarin Cryptocurrencies

- Osinbajo ya ce bai kamata CBN ya hana mu’amala da wannan kudi a kasar ba

- A maimakon a haramta amfani da tsarin, ya ce ya kamata hukuma ta sa ido ne

Daya daga cikin ‘ya ‘yan mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo mai suna Fiyin Osinbajo, ya yi dogon rubutu a game da tsarin Cryptocurrencies.

Fiyin Osinbajo ya bayyana yadda Duniya ta karbi wadannan kudin yanar gizo watau Cryptocurrencies, duk da cewa babu wata hukuma mai kula da shi.

A cewar Fiyin Osinbajo, saboda farin-jinin da wannan kudi ya yi a ‘yan shekarun bayan nan wajen musaya da cinikin kaya, darajar Crypto ta zarce Dala tiriliyan 1.

Osinbajo ya ce za a iya amfani da wannan tsarin yanar gizo wajen aika kudi daga kasa zuwa kasa cikin sauki, ba tare da bata lokaci ba, kuma a farashi mai matukar araha.

KU KARANTA: Cryptocurrencies: An kai karar babban bankin Najeriya CBN da SEC kotu

Rubutun ‘dan mataimakin shugaban kasar ya yi bayani a game da yadda al’umma su ka rungumi fasahohin zamani wajen samun abin yi da rage talauci, har a Najeriya.

Bincike ya nuna cewa an yi cinikin kimanin Naira biliyan 100 na cryptocurrency a Najeriya a shekarar 2020 kurum, wannan ya nuna karbuwar tsarin inji marubucin.

Tsoron da gwamnan CBN ya ke ji shi ne ana amfani da Cryptocurrencies wajen yin barna tun da ba a sanin wadanda su ke mu’amala da wannan kudi a kafofin yanar gizo.

Mista Fiyin Osinbajo ya ce matakin da CBN ya dauka zai yi tasiri wajen nakasa tattalin arzikin Najeriya ta hanyoyi da-dama, daga ciki har da jawo asarar biliyoyin kudi.

Cryptocurrency: ‘Dan Osinbajo ya rubutawa CBN takarda, ya soki matakin da aka dauka
Fiyin Osinbajo Hoto: www.pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Za a karkare aikin hanyar Abuja zuwa Kano a farkon 2023

Marubucin ya ce kudin da su ke shigo wa Najeriya daga ketare zai ragu dalilin haka. Osinbajo ya ce kamata ya yi hukuma ta sa ido, a maimakon ta dauki matakin haramci.

Kwanakin baya ne aka ji babban bankin CBN na kasa ya haramta duk mu’amalar Cryptocurrencies.

CBN ta ce ana amfani da kudin Cryptocurrencies wajen harkokin ta’addanci. Bankin ya ce wasu Ana sayen mugayen makamai da miyagun kwayoyi ta hanyar wannan kudi.

Jami'in CBN da ya bada wannan sanarwa ya ce hana ma’amala da wannan kudi ba zai kawo matsalar tattalin arziki ba domin akwai wasu kafofin hada-hada na fasaha.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki.

Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai (Info Mgt), kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel