CBN ta ce ana amfani da kudin Cryptocurrencies wajen harkokin ta’addanci

CBN ta ce ana amfani da kudin Cryptocurrencies wajen harkokin ta’addanci

- CBN ya ce aika-aikan da ake yi ta sa aka hana amfani da cryptocurrencies.

- Bankin kasar ya ce miyagu suna amfani da wannan kudi wajen ta’addanci

- Ana sayen mugayen makamai da miyagun kwayoyi ta hanyar wannan kudi

A ranar Lahadi, Babban bankin Najeriya na CBN ya fito da jawabi, ya kare matakin da ya dauka na haramta amfani da kudin cryptocurrencies.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa bankin CBN ya yi magana ne ta bakin mukaddashin mataimakin darektan sadarwa, Osita Nwanisobi.

CBN ya bayyana cewa hana ma’amala da wannan kudi ba zai kawo matsalar tattalin arzikin kasa ba domin akwai wasu kafofin hada-hada na fasaha.

A jawabin na sa, Osita Nwanisobi, ya bayyana cewa babu mai lura da ‘Cryptocurrencies’, sannan babu wanda ya ba irin wadannan kudi lasisin aiki.

KU KARANTA: An hana cinikin Bitcoins da takwarorinsa - CBN

Nwanisobi ya ce wadannan dalilai su ka sa babban bankin kasar ya haramta amfani da su, domin sun ci karo da nauyin da aka daura wa bankin CBN.

“A kan menene mutum zai boye ta karkashin cryptocurrencies, ya rika cinikinsa.” Inji Nwanisobi.

“An koma ana amfani da cryptocurrencies wajen yin aika-aika irir-iri wadanda su ka hada da safarar miyagun kudi, ta’addanci da sayen makamai.”

Har ila yau, Nwanisobi ya ce bayan munanan ayyuka na ta'addanci, an gano wasu su na amfani da wannan kudi domin guje wa biyan haraji a Najeriya.

KU KARANTA: Farashin litar man fetur zai iya kai wa N200 kwanan nan

CBN ta ce ana amfani da kudin Cryptocurrencies wajen harkokin ta’addanci
Gwamnan babban banki Hoto: www.ft.com
Asali: UGC

“Amfani da cryptocurrencies da ake yi wajen sayen manya da miyagun kwayoyi a boyayyen shafin yanar gizon da ake kira ‘Silk Road’, sanannen abu ne.”

“Bankuna da dama da masu zuba hannun jari sun raba kansu da cryptocurrencies, saboda barnar da ake yawan tafkawa da wannan kudi.” Inji bankin CBN.

A jiya ne mu ka ji cewa ashe hukumar FBI ta kasar Amurka ce ta ankarar da gwamnatin tarayya cewa ana tafka ta'adi da kudin cryptocurrencies a Najeriya.

Wata majiya ta bayyana cewa 'yan damfara su na shigo da tsakanin $200m zuwa $300m zuwa cikin Najeriya a kowane mako, don haka aka dauki mataki.

Jami'an FBI sun ce 'yan damfarar nan da ake kira 'Yahoo Boys su kan yi amfani da cryptocurrencies.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel