Cryptocurrencies: An kai karar babban bankin Najeriya CBN da SEC gaban Alkali
- An samu kungiyar da ta kai karar CBN saboda hana cinikin ‘Cryptocurrencies’
- Digital Rights Lawyers Initiative ta ce wannan mataki da aka dauka ya saba doka
- Kungiyar ta ce a baya CBN ta amince da hada-hada ta hanyar Cryptocurrencies
Wata kungiya mai zaman kanta wanda ake kira Digital Rights Lawyers Initiative, ta na kalubalantar hana amfani da cryptocurrencies da aka yi.
Jaridar Punch ta ce Digital Rights Lawyers Initiative ta shigar da karar babban bankin Najeriya watau CBN da hukumar SEC a kotu a kan wannan lamari.
Rahoton ya bayyana cewa an shigar da karar mai lamba FHC/L/CS/ 188/2021 ne a ranar Litinin, 8 ga watan Fubrairu, 2021 a babban kotun tarayya na Legas.
Kungiyar lauyoyin na Digital Rights Lawyers Initiative ta na tuhumar bankin CBN da hukumar SEC mai alhakin kula da sha'anin hannun jari a Najeriya.
KU KARANTA: Kasar Amurka ta ankarar da CBN kan barnar da ake yi da Bitcoins
A cewar kungiyar, CBN ta fitar da sanarwa a 2020, inda ta amince da kudin cryptocurrencies a matsayin dukiyar da ta halatta ayi kasuwanci da ita a kasar.
A dalilin haka lauyoyin da su ka tsaya wa wannan kungiya su ka bukaci kotu ta yi watsi da sabuwar dokar da CBN ta kawo na haramta mu’amala da kudin.
Har ila yau, lauyar da ta tsaya wa kungiyar, Irene Chukwukelu, ta roki kotu ta hana bankin CBN tsoma baki game da sha’anin kudin cryptocurrency a Najeriya.
Irene Chukwukelu ta na ikirarin cryptocurrency ya samu wuri a sashe na 44 na dokar kasa. Sannan ta nemi tabbatar da dokar Investments & Securities ta 2007.
KU KARANTA: Patience Jonathan za ta san matsayar dukiyarta a Kotu
Kawo yanzu kotu ba ta zabi Alkalin da zai saurari wannan kara da aka shigar a farkon mako ba. Daga nan ne kungiyar za ta san lokacin da za a saurari wannan kara.
A makon da ya gabata kun ji cewa CBN ta ce ana amfani da kudin Cryptocurrencies wajen harkokin ta’addanci, don haka ta haramta amfani da su a kasar nan.
Bankin kasar ya ce miyagu suna amfani da wannan kudi wajen sayen mugayen makamai da miyagun kwayoyi, wanda hakan ke kara jefa al'umma a cikin hadari.
CBN ya bayyana cewa hana ma’amala da wannan kudi ba zai kawo matsalar tattalin arziki ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng