A duba aikin da kwamitin El-Rufai ya yi – Shugabannin K/Yamma ga Buhari

A duba aikin da kwamitin El-Rufai ya yi – Shugabannin K/Yamma ga Buhari

-Jiga-jigan APC daga Kudu maso yamma suna so a duba aikin kwamitin El-Rufai

-Kwanakin baya Nasir El-Rufai ya yi aiki game da yi wa tsarin mulki garambawul

-Shugabannin Yarbawa suna so a aika wa Majalisa rahoton wannan aikin da aka yi

Shugabannin jam’iyyar APC da su ka fito daga yankin Kudu maso yammacin Najeriya suna so a kakkabe aikin da wani kwamiti na Nasir El-Rufai ya yi.

Kwanakin baya ne aka zabi Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya jagoranci kwamitin yi wa sha’anin mulki da shugabancin Najeriya garambawul.

Tun daga lokacin da wannan kwamiti ya yi aikinsa ya gama, ba a sake jin labarin rahotonsa ba. Jaridar The Nation ta ce an sake dawo da maganar a yanzu.

Jagororin APC na yankin Yarbawa sun kai wa mai girma Muhammadu Buhari rokonsu na a duba wannan aiki da aka yi, domin a dabbaka wasu shawarwarin.

KU KARANTA: Lokaci ya yi da ya kamata a duba kwakwalwar Buhari – Ezekwesili

Manyan APC da su ka hadu da shugaban kasar a kan wannan maganar su ne: Bisi Akande, Aremo Olusegun Osoba, Dr. Yomi Finnih da Prince Tajudeen Olusi.

Shahararrun ‘yan siyasar sun nemi shugaban kasa ya aika rahoton kwamitin zuwa ga majalisar tarayya wajen aiki da shi ayi wa tsarin mulki kwaskwarima.

A cewar manyan, wannan shi ne ra’ayin mafi yawan jama’a da ke goyon a sake wa Najeriya fasali.

Akande, ya yi gwamna a 1983 kuma shi ne wanda ya fara rike jam’iyyar APC bayan an kafa ta

KU KARANTA: Zan yi wa Tinubu ritaya - George

A duba aikin da kwamitin El-Rufai ya yi – Shugabannin K/Yamma ga Buhari
Bisi Akande a fadar Shugaban kasa Hoto: dailypost.ng
Source: Twitter

Haka zalika Osoba ya yi gwamna a jihar Ogun, shi kuwa Olusi, tsohon ‘dan majalisa ne kuma ya taba rike kwamishina da kujerar shugaban jam’iyya a ACN.

Finnih, kamar sauran ya na cikin jagororin jam’iyyar APC a Kudu maso yammacin Najeriya.

Kwanakin baya Bode George ya yi magana game da ziyarar Bisi Bisi Akande, Aremo Olusegun Osoba, Dr. Yomi Finnih da Prince Tajudeen Olusi zuwa Aso Villa.

Jagoran jam'iyyar PDP mai hamayya ya ce Bola Tinubu ne ya tura 'yan siyasar wajen shugaba Buhari, ganin cewa tsohon gwamnan ba ya nan aka yi zaman.

Da ya ke magana, tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar na PDP ya ce akwai bukatar Tinubu ya biya bashin makudan kudin da ya wawushe daga aljihun jihar Legas.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel