Jam'iyyar APC na harin samun sababbin mambobi miliyan 2 a Adamawa

Jam'iyyar APC na harin samun sababbin mambobi miliyan 2 a Adamawa

- A ci gaba da rajistar sababbin mambobi na jam'iyyar APC, jam'iyyar na harin samun mutane miliyan 2 a Adamawa

- Farfesa Tahir Mamman ya bayyana bukatar jam'iyyar na samun mambobin domin tunkarar zaben 2023

Shugaban jam'iyyar na jihar Adamawa ya bukaci jami'an tsaro da su gujewa siyasa wajen gudanar da ayyukansu lokacin rajistar

Jam’iyyar APC ta ce tana shirin yin rajistar mambobi miliyan 2 a Adamawa a ci gaba da rajistar membobin da ke gudana a duk fadin kasar, Vanguard ta ruwaito.

Farfesa Tahir Mamman, memba Mai Kula da Kwamitin Shirye-shiryen Babban Taro na APC ya fadi haka ne a wani taron manema labarai ranar Asabar a Yola.

KU KARANTA: Chasun Badala: Kaduna ta gurfanar da kakakin PDP tare da wasu da laifin yunkurin aikata badala

Jam'iyyar APC na harin samun sababbin mambobi miliyan 2 a Adamawa
Jam'iyyar APC na harin samun sababbin mambobi miliyan 2 a Adamawa Hoto?: Vanguard
Source: Facebook

“Muna so mu ga akalla mazauna Adamawa miliyan biyu a matsayin mambobi masu rajista na jam'iyyar APC a cikin rajistar membobin da ke gudana.

"Da yardar Allah a 2023, zai zama APC 'SAK' a dukkan matakan Tarayya, Jiha har zuwa Kananan Hukumomi (LGAs)," in ji shi.

Mamman ya ce tun farko jam'iyyar ta shirya Mega Rally a jihar don karbar wasu fitattun mutane da suka sauya sheka daga wasu jam'iyyun, amma dole ta fasa taron saboda cutar COVID-19.

Shima da yake jawabi, Sanata Isiyaku Abbo, mai wakiltar Yola ta Arewa, wanda ya sauya sheka daga PDP zuwa APC ya ce sauya sheka da yayi don bukatun mutane ne, yana mai cewa bai fita domin ya yanke kauna ba ne.

Abo ya bukaci hukumomin tsaro a jihar da su nisanta kansu da siyasa yayin gudanar da ayyukansu don tabbatar da adalci.

KU KARANTA: Pantami: Shin za a rufe layin wadanda basu hada SIM dinsu da NIN ba?

Mista Ibrahim Bilal, shugaban jam'iyyar APC na jihar, ya bukaci magoya bayan jam'iyyar da masu biyayya da su tabbatar sun yi rajista a mazabunsu a duk fadin jihar don tabbatar da nasarar aikin.

A wani labarin, Wata babbar kotun tarayya dake zaune a Abuja ta yi watsi da karar amfani da kwalin jabu da jami'yyar All Progressives Congress APC ta shigar kan gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki.

Alkali Ahmed Mohammed ya yi watsi da karar nan ranar Asabar, Channels TV ta ruwaito.

APC da wani jigon APC Edobor, sun shigar da karan cewa gwamna Obaseki ya yi amfani da takardan bogi yayinda yake neman takaran gwamnan jihar da akayi ranar 19 ga Satumba, 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel