Buhari: Abin kunya ne Gwamnoni har 10 su yi zuga, su tafi Daura inji Afenifere, PDP

Buhari: Abin kunya ne Gwamnoni har 10 su yi zuga, su tafi Daura inji Afenifere, PDP

- PDP ta zargi Gwamnonin jam’iyyar APC da watsi da aikinsu, su tafi garin Daura

- Gwamnoni 10 ne su ka bar gida domin ganin Buhari ya na sabunta rajistar APC

- Kungiyar Afenifere da Junaid Mohammed duk sun soki wadannan Gwamnonin

Punch ta ce Jam’iyyar hamayya ta PDP da kungiyar nan ta Afenifere, sun soki tafiyar da gwamnonin jam’iyyar APC goma su kayi zuwa garin Daura.

Gwamnonin sun yi watsi da aikin da ke gabansu, sun raka shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa mahaifarsa Daura, inda ya jaddada rajistar APC.

Jam’iyyar PDP mai adawa ta fitar da jawabi ta bakin sakatarenta na yada labarai na kasa, Kola Ologbondiyan, inda ta zargi gwamnonin da gantali.

“Karshen rashin sanin abin da ya kamata ne. Abin ya wuce hankali, ace gwamnoni sun bar aikinsu na mulki a lokacin da ake fama da babbar matsalar tsaro da matsin tattalin arziki, su tafi gantali.”

KU KARANTA: An samu baraka a APC a Jihar Katsina yayin da Shugaba Buhari ya ke Daura

Ya ce: “Da ace za su iya irin wannan kokari wajen ainihin shugabanci a jihohinsu, da ba mu yi fama da garkuwa da mutane, fashi da makami, hare-haren ‘yan bindiga, da sauran laifuffuka ba.”

“A kan menene kusan gwamnoni 10 za su yi watsi da jihohinsu, saboda kurum su shaida shugaban kasa ya na sa hannu a rajista. Yaushe gwamnonin nan su ka kaddamar da wani aiki?”

Yinka Odumakin na kungiyar Afenifere ya shaida wa ‘yan jarida cewa gwamnonin sun nuna ba su da aikin yi, idan za su iya yi wa Buhari rakiyar yin rajista.

“Da ace su na da wani abin yi, da ba za su biye wa wannan tarkacen ba.” Inji Yinka Odumakin.

KU KARANTA: Buhari zai je Daura, ya yi aikin rajistar APC

Buhari: Abin kunya ne Gwamnoni har 10 su yi zuga, su tafi Daura inji Afenifere, PDP
Buhari da Gwamnoni 10 a Daura Hoto: Facebook Daga: Femi Adesina
Source: Facebook

Tsohon ‘dan majalisar wakilan Najeriya, kuma dattijon Arewa, Dr. Junaidu Mohammed, ya yi tir da wannan lamari, ya ce gwamnonin ba su san ya kamata ba.

A ranar Juma'a ku ka ji cewa Buhari ya bar Abuja, ya isa garin Daura domin rajistar Jam’iyyar APC.

Gwamna Aminu Bello Masari da mataimakinsa, Munir Yakubu, da shugaban majalisar dokokin Katsina, da Alkalin Alkalan jihar su ka tarbi Buhari a Katsina.

Gwamnoni 10 a karkashin jagorancin Mai Mala Buni da kuma irinsu Ahmad Lawan, Ken Nnamani; da wasu manyan APC su na garin Daura a yanzu haka.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel