Wasu ‘Yan APC sun bangare, sun fito da tafiyar 'APC Pressure Group' a Katsina

Wasu ‘Yan APC sun bangare, sun fito da tafiyar 'APC Pressure Group' a Katsina

- Kungiyar APC Pressure Group ta bayyana a Katsina a karshen makon nan

- Wasu ‘Ya ‘yan jam’iyya sun bangare, sun zargi wasu da nuna son kai a APC

- Daga cikin wadanda su ke cikin tafiyar, har da hadimin Gwamnan Katsina

Rahotanni daga jaridar Katsina Post sun tabbatar da cewa abubuwa ba su tafiya daidai a cikin jam’iyyar APC mai mulki a jihar Katsina.

Jaridar ta fitar da rahoto a ranar Lahadi, 31 ga watan Junairu, 2021, cewa an samu bayyanar wasu ‘yan taware a tsakanin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC a Katsina.

Kamar yadda mu ka samu labari, wadannan ‘yan taware sun kira kansu APC Pressure Group.

‘Yan bangaren na APC Pressure Group sun gudanar da taronsu na farko a filin wasa na Ahmad Musa Sport Center da ke jihar Kano, a ranar Lahadin nan.

KU KARANTA:

A wani faifen bidiyo, an ga ‘ya ‘yan wannan kungiya da su ka halarci taron da aka yi a garin Kano.

Dga cikin wadanda su ka halarci wannan taro na ‘yan taware har da wasu wadanda ke rike da mukaman siyasa a gwamnatin Rt. Hon. Aminu Bello Masari.

Haka zalika a wani faifen bidiyon na dabam, an hangi mai ba gwamnan Katsina shawara a wajen muradinsa, Alhaji Sabo Musa, ya na kira ga mai gidan na sa.

Alhaji Sabo Musa ya roki mai girma gwamna Aminu Bello Masari, ya yi wani abu tun wuri domin a hana jam’iyyar APC ta reshen jihar Katsina ta saki hanya.

KU KARANTA: Sanata Hanga ya bayyana matsayar Tinubu a APC a zabe mai zuwa

Wasu ‘Yan APC sun bangare, sun fito da tafitar 'APC Pressure Group' a Katsina
Oishin APC Hoto: www.katsinapost.com.ng
Source: UGC

“Ba za mu saba dokar jam’iyya ba, amma za mu cigaba da huro wuta domin ayi abin da ya dace. Muna kira ga gwamna Masari ya tabbatar an yi abin da ya dace.”

Musa ya zargi wasu tsirarun masu son kai da yunkurin kawo matsala a tafiyar jam’iyyar APC a Katsina. Hakan na zuwa ne a lokacin da ake kokarin dinke baraka.

Ku na da labari cewa a ranar Asabar da ta gabata ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya sabunta rijistarsa ta zama cikakken 'dan jam'iyyar APC a Katsina.

A nan ne shugaban kasa ya ce APC ba zata kara daurewa wani 'dan takara gindi daga Abuja ba.

Da yake magana da manema labarai a garin Daura, shugaba Buhari ya bada tabbacin cewa lokacin cusa wa al'umma 'yan takara daga birnin tarayya Abuja ya kare.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel