Da Dumi-Dumi: Yan Sanda Sun Harbawa Matasa Barkonon Tsohuwa A Lekki Tollgate, Bidiyo

Da Dumi-Dumi: Yan Sanda Sun Harbawa Matasa Barkonon Tsohuwa A Lekki Tollgate, Bidiyo

  • Matasa na gudanar da gangamin tunawa da zanga-zangar EndSARS bayan shekaru biyu
  • Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa don fatattakar matasan da ke gudanar da tattaki a Lekki Tollgate
  • A ranar 20 ga watan Oktoban 2020 ne matasa suka gudanar da zanga-zangar neman a kawo karshen yan sandan SARS lamarin da ya zama rikici

Lagos - Jami’an rundunar yan sandan Najeriya sun harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa matasan da ke bikin tunawa da zanga-zangar #EndSARS a Lekki tollgate.

Jaridar TheCable ta rahoto cewa an shirya gangamin ne domin cikar shekaru biyu da gudanar da gangamin EndSARS.

Lekki tollgate
Da Dumi-Dumi: Yan Sanda Sun Harbawa Matasa Barkonon Tsohuwa A Lekki Tollgate Hoto: TheCable
Asali: UGC

A safiyar yau Alhamis, 20 ga watan Oktoba ne matasa suka taru a yankin tollgate suna ta wake-wake yayin da suke rike da akwatin gawa don tunawa da lamarin da ya afku a ranar 20 ga watan Oktoban 2020.

Kara karanta wannan

An Yi Kazamin Arangama Tsakanin Yan Tasha Da Yan Kasuwa, Ana Fargabar Rasa Rayyuka

Gangamin wanda aka yiwa lakabi da ‘tattakin lumana’ ya dauki sabon salo yayin da jami’an yan sanda suka harba barkonon tsohuwa domin fatattakar wadanda ke tattakin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kakakin yan sandan jihar Lagas, Benjamin Hundeyin, ya fada ma Channels TV cewa wasu daga cikin masu tattakin basu bi doka ba sannan sun dare saman tollgate.

Ya ce:

“Babu bukatar aikata haka. Kuna tattaki, kawai ku yi tafiyarku. Amma sai wadannan mutanen suka tsaya a wajen sannan suka dare saman tollgate, sun zama masu hayaniya, suna barazanar karya doka da oda da ke kasa.
“Ba za mu tsaya a nan muna kallonsu suna rashin da’a ba. Abu mafi sauki da za mu iya yi shine amfani da barkonon tsohuwa, duk wani abu baya ga barkonon tsohuwar zai zama mai cutarwa.
“Ba a samu wanda ya ji rauni ba. Kawai aikinmu muka yi sannan muka fuskanci wadanda suka nuna rashin da’a.”

Kara karanta wannan

Yan Mata 2 Sun Kayar Da Gardawa 4 Wajen Gasar Cin Malmalan Sakwara

Ga bidiyon a kasa:

‘Yan Bindiga Sun Halaka Dan Sanda Da Wasu 22 Sannan Suka Kona Gidaje 50 A Wata Jahar Arewa

A wani labari na daban, ‘Yan bindiga sun halaka mutum 23 ciki harda wani jami’in dan sanda sannan suka jikkata mutum 11 yayin da suka kai farmaki garin Gbeji da ke karamar hukumar Ukum ta jihar Benue.

Maharan sun kai mummunan harin ne a ranar Laraba, 19 ga watan Oktoba, jaridar Leadership ta rahoto.

Mai ba gwamnan jihar shawara ta musamman kan harkokin tsaro, Lt Col. Paul Hembah (rtd), wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce dan sandan wanda ya ji mummunan rauni ya mutu ne a hanyar zuwa asibiti.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel