WTO: Najeriya za ta tsaya wa Ngozi Okonjo-Iweala inji Gwamnatin Tarayya

WTO: Najeriya za ta tsaya wa Ngozi Okonjo-Iweala inji Gwamnatin Tarayya

- Gwamnatin Najeriya ta yi magana game da takarar Ngozi Okonjo-Iweala

- Okonjo-Iweala ta samu goyon bayan mafi yawan kasashe a takarar WTO

- Najeriya ta ce ta na sa ran cewa ‘yar takararta ta zama shugabar kungiyar

Gwamnatin tarayya ta sha alwashin tabbatar da cewa ‘Yar Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala ta zama sabuwar shugabar kungiyar WTO, inji Daily Trust.

Jaridar ta fitar da wannan rahoto a ranar Alhamis, 30 ga watan Oktoba, 2020, ta ce ma’aikatar harkokin kasasashen wajen Najeriya ta bayyana haka.

Mai magana da yawun bakin ma’aikatar tarayyar, Mista Ferdinand Nwonye, ya bayyana cewa Najeriya za ta tsaya wa takarar Dr. Ngozi Okonjo-Iweala.

KU KARANTA: Zan kai labari - Ngozi Okonjo-Iweala

Ferdinand Nwonye ya fitar da wani jawabi da ya yi wa take da “Update on Ngozi Okonjo-Iweala’s aspiration to lead the World Trade Organization.”

“Inda aka kwana game da burin Ngozi Okonjo-Iweala na jan ragamar kungiyar kasuwanci, WTO.”

Nwonye ya na cewa:

“Najeriya za ta cigaba da tattauna wa da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa burin ‘yar takararta na rike shugabancin WTO ta tabbata."

"Ma’aikatar harkokin waje ta na sa ranar da cewa an yi zabe na uku, kuma na karshe na fito da Darekta-Janar na kungiyar kasuwancin Duniya a ranar Talata, 27 ga watan Oktoba, 2020, kuma an fitar da sakamako a ranar Laraba, 28 ga watan Oktoba, 2020.”

KU KARANTA: Kotu ta ki ba EFCC damar cafko Alison-Madueke daga kasar waje

WTO: Najeriya za ta tsaya wa Ngozi Okonjo-Iweala inji Gwamnatin Tarayya
Ngozi Okonjo-Iweala da Myung-hee Hoto: www.bbc.com/pidgin
Asali: UGC

Ya ce: “’Yar takarar da ta fito daga Najeriya, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta samu rinjayen kasashe, amma ba a bayyanata a matsayin wanda ta yi nasara ba tukuna.”

A karshe jawabin ya ce: “Ya kamata a san Okonjo-Iweala ta samu goyon bayan mafi yawan yankuna, inda Amurka ce kawai ta ke mubaya’ar yi mata adawa.”

A baya kun ji cewa gwamnatin kasar Amurka ta fito karara ta nuna sam ba ta goyon bayan Ngozi Okonjo-Iweala a neman takarar shugaban kujerar kungiyar WTO.

Amurka ta ce Ministar Koriya ta Kudu, Yoo Myung-hee ta san aiki, shiyasa ta ke mara mata baya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel