WTO: Myung-hee ta san aiki, shiyasa mu ke mara mata baya inji Amurka

WTO: Myung-hee ta san aiki, shiyasa mu ke mara mata baya inji Amurka

- Amurka ta fito karara ta nuna ba ta goyon bayan Ngozi Okonjo-Iweala a WTO

- Gwamnatin Trump ta fi karkata wajen Ministar kasar Koriya, Yoo Myung-hee

- Okonjo-Iweala ta yi aiki a bankin Duniya, akidunta sun sha ban-bam da Trump

Yayin da kafar Dr. Ngozi Okonjo-Iweala daya ta ke kan kujerar kungiyar WTO, kasar Amurka ta fito ta nuna adawarta ga mutumiyar Najeriyar.

Gwamnatin kasar Amurka ba ta tare da Ngozi Okonjo-Iweala, ta na goyon bayan Yoo Myung-hee ne a zaben wannan kungiya ta kasuwancin Duniya.

Kungiyar EU da takwararta AU ta Afrika da sauran manyan kasashen Duniya su na goyon bayan Okonjo-Iweala, Amurka ce kurum babban kalubalanta.

Wasu na ganin cewa Amurka ta na yi wa Yoo Myung-hee sha’awar wannnan kujera ne saboda kokarinta da aka gani a gwamnatin Koriya ta Kudu.

KU KARANTA: Jerin ‘Yan Najeriya da su ka samu manyan mukamai a mulkin Buhari

Yoo Myung-hee ta na da kyakkyawar alaka da gwamnatin Amurka a karkashin Donald Trump.

Kasar Amurka ta ce ta na goyon bayan Yoo Myung-hee ta rike wannan kujera ne domin rikakkar masaniya ce a kan sha’anin kasuwanci a Duniya.

Amurka ta ce Myung-hee ta nuna hakan a shekaru 25 da ta yi ta na aiki. Jaridar Premium Times ta ce ma’aikatar kasuwancin kasar ta bayyana wannan.

A ra’ayin mahukuntan Amurka, Ministar Koriyar ta cancanci ta ja ragamar WTO domin ta na da duk abin da ake bukata na zama shugabar kungiyar.

Jawabin ya ce: “Wannan mawuyacin lokaci ne ga kungiyar WTO da harkar kasuwancin Duniya.”

KU KARANTA: Najeriya da Okonjo-Iweala su na daf da sanin matsayarsu a WTO

WTO: Myung-hee ta san aiki, shiyasa mu ke mara mata baya inji Amurka
Dr. Ngozi Okonjo-Iweala Hoto: www.bbc.com/pidgin
Asali: UGC

Ko da Amurka ba ta yi magana kan Okonjo-Iweala ba, ta nuna ta fi karkata a kan wanda ta ce ta san aiki. Amma ita ma ‘yar Najeriyar ba kanwar lasa ba ce.

Dr. Okonjo-Iweala ta yi karatu ne a manyan jami’oin Duniya, kuma ita ce macen farko da ta fara zama Ministar tattalin Najeriya, ta rike matsayin sau biyu.

Ana tunanin akidar Okonjo-Iweala da ta yi aiki a bankin Duniya, ba za ta zo daya da ta Donald Trump wanda ya ke zargin kungiyar WTO da fifita kasar Sin ba.

A jiya kun ji cewa tsohuwar ministar kudin Najeriya, Dr. Ngozi Okonjo Iweala na daf da zama sabuwar shugabar kungiyar kasuwanci na duniya, WTO.

Kasashen Turai ba su tare da Yoo Myung-hee, wanda gwamnatin Amurka ta ke mara wa baya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel