An yi awon gaba da matafiya yan Kano 18 a jihar Kogi

An yi awon gaba da matafiya yan Kano 18 a jihar Kogi

- Yan kasuwa sun shiga hannun azzalumai a hanyarsu ta zuwa kasar igbo

- Akalla mutan jihar Kano 18 ake zargin anyi awon gaba da su a Kogi

- Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan sun bukaci kudin fansa

Wasu yan bindiga a jihar Kogi sun kwashe matafiya yan kasuwa daga jihar Kano wadanda ke hanyarsu ta zuwa jihar Abia, kudu maso gabashin Najeriya.

Yan kasuwan, dukkansu yan Kantin Kwari, na hanyar tafiya Aba ne a jihar Abia domin siyayyarsu yayinda yan bindiga suka far musu kuma suka shiga da su cikin daji, Daily Trust ta ruwaito.

Dirakta manajan kasuwar Kantin Kwari, Alhaji Abba Bello, ya tabbatar da hakan.

A cewarsa, "Mutanen da aka sace su 18 ne, amma kawo yanzu mun samu sunayen 12, amma muna kyautata zaton su 18 ne."

"Suna kan hanyar tafiya Aba a Abiya yayinda yan bindiga suka taresu a hanyar Lokoja-Okene a jihar Kogi."

Alhaji Bello ya ce har yanzu bai samu labari ko yan bindigan sun tuntubi iyalan wadanda aka sace don bukatan kudin fansa ba.

Amma wasu majiyoyi sun bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun bukaci milyan 50 amma daga baya suka amince da karban milyan 27.

KU KARANTA: Hadarin hanyar Bauchi ya yi sanadiyyar rayukan mutane 21 daga cikin fasinjoji 22 - FRSC

An yi awon gaba da matafiya yan Kano 18 a jihar Kogi
An yi awon gaba da matafiya yan Kano 18 a jihar Kogi
Asali: UGC

KU DUBA: Cikin kwanaki 10, kimanin mutane 13,000 suka kamu da Korona

A wani labarin kuwa, 'yan bindiga sun yi awon gaba da mutane goma sha takwas da suka hada da wasu masu jego guda biyu a wani harin tsakar dare da suka kai a Mando da ke yankin karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Mazauna garin sun sanar da cewa 'yan bindiga sun dira kauyen dauke da bindigu kirar AK47 tare da yin bincike gida gida domin neman kayan abinci, kamar yadda TVC ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne a tsakar daren ranar Talata zuwa safiyar ranar Laraba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel