'Yan bindiga sun yi awon gaba da masu jego hudu da sauran wasu mutane 14 a Kaduna

'Yan bindiga sun yi awon gaba da masu jego hudu da sauran wasu mutane 14 a Kaduna

- Wasu 'yan bindiga sun kai hari garin Mando a Birnin Gwari tare da sace mutane 18 da suka hada da mata masu jego guda hudu

- 'Yan bindigar sun kai harin ne a yayin da jama'a ke jin dadin zaman lafiyar da aka samu bayan ragargazar 'yan bindiga a hanyar Birnin Gwari zuwa Funtua

'Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane goma sha takwas da suka hada da wasu masu jego guda biyu a wani harin tsakar dare da suka kai a Mando da ke yankin karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Mazauna garin sun sanar da cewa 'yan bindiga sun dira kauyen dauke da bindigu kirar AK47 tare da yin bincike gida gida domin neman kayan abinci, kamar yadda TVC ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne a tsakar daren ranar Talata zuwa safiyar ranar Laraba.

A wani jawabi mai dauke da sa hannun Barista Salisu Haruna, shugaban cigaban masarautar Birnin Gwari (BEPU), ya bayyana cewa 'yan bindigar sun yi awon gaba da dukiyar miliyoyin Naira daga gidajen jama'a.

KARANTA: Faifan bidiyon sabuwar wakar Hausa ya fusata Hausawa a dandalin sada zumunta

"An samu kwanciyar hankali a kan hanyar Birnin Gwari zuwa Funtua sakamakon atisayen jami'an tsaro a 'yan kwanakin da suka gabata.

"Ana cikin jin dadin samun wannan nasara ne sai gashi wasu 'yan bindiga sun kai hari kauyen Mando, mai nisan kilomita biyar daga garin Birnin Gwari.

'Yan bindiga sun yi awon gaba da masu jego hudu da sauran wasu mutane 14 a Kaduna
'Yan bindiga sun yi awon gaba da masu jego hudu da sauran wasu mutane 14 a Kaduna
Source: Twitter

"A sabon harin, wanda 'yan bindigar suka kai da misalin karfe 1:30 na safiyar ranar Laraba tare da yin garkuwa da mutane goma sha takwas, wadanda suka hada da mata masu jego guda hudu," a cewar jawabin.

KARANTA: Tsohon kwamishinan Ganduje: Wasu tantirai kuma jahilai ke sarrafa akalar gwamnatin Kano

"Sun shiga gida - gida tare da yin awon gaba da kayan abinci da sauran kayan jama'a da ya zuwa yanzu ba'a kama kididdigar kudinsu ba.

"Bayan sun sace mata masu jegon tare da jariransu, sun yi awon gaba da wasu sauran mutane goma dukkansu maza.

"Muna kira ga jami'an tsaro, musamman rundunar sojin sama da ke da sansani a Birnin Gwari daura da garin Mando, da su dauki matakin gaggawa domin kare rayuwar jama'a da dukiyoyinsu."

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa jarumar Kannywood, Rahama sadau, na fuskantar sabuwar caccaka daga masoyanta Musulumai bayan ta sake sakin wani hotonta a dandalin sada zumunta.

Mabiyan jarumar a shafinta na Tuwita sun mayar mata da martani kan hoton da ta ɗauka da jarumar masana'antar Bollywood, Shabnam Surayyo.

Sai dai jarumar ta dawo shafinta na Tuwita ta wallafa wata magana da Priyanka Chopra ta taba yi akan jajiracewa yayin fuskantar suka da tsangwama.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel