Shekaru 5 ina sayarwa mutane mushen kaji a Maiduguri, Ebere

Shekaru 5 ina sayarwa mutane mushen kaji a Maiduguri, Ebere

- Hukumar NSCDC ta cika hannu da wani mai sayar da mushen kaji

- Mutumin ya kwashe shekara da shekaru yana yaudarar masu gidan abinci

- Ya bayyana cewa ya shiga yin haka ne tun lokacin da mahaifinsa ya rasu

Wani mutum mai suna, Hassan Ebere, ya bayyana yadda ya sayar da mushen kaji sama da 6,000 ga al'ummar Maiduguri tsawon shekaru biyar yanzu domin neman kudin ciyar da kansa.

Ebere ya bayyana hakan ne yayin magana da kamfanin dillancin labarai (NAN), bayan jami'an NSCDC suka damkeshi ranar Laraba a jihar Borno.

"Na kan je rafin Ngadabul, bayan gidan talabijin BRTV, inda nike daukan mushen kajin da gidajen gona suka jefar, " ya bayyana.

"Kowani mako, na kan dauki guda goma ko fiye da haka, sannan in gyara kuma in sayarwa mutane."

"Kasuwannin da nake sayarwa sune kasuwar Kifin Baga, kasuwar Monday Market, shagunan masu Suya, da gidajen abinci, a cikin gari."

"N700 zuwa N800 nike sayarwa. Amma idan suka kai yan kwanaki (ban sayar ba), na kan kai gidajen giya a bayan Ngomari in sayar da su N250," ya kara.

Ebere ya ce shaidan ne ya tura shi aikata wannan abu kuma yana rokon a yafe masa.

Shugaban hukumar NSCDC na jihar Borno, Abdullahi Ibrahim, ya ce an damke mutumin ne yayinda yake gyaran kajin a bayan gidan talabijin da rediyo na BRTV ranar 2 ga Junairu, 2021

Kalli Hotunan:

Shekaru 5 ina sayarwa mutane mushen kaji a Maiduguri, Ebere
Shekaru 5 ina sayarwa mutane mushen kaji a Maiduguri, Ebere
Source: Facebook

Shekaru 5 ina sayarwa mutane mushen kaji a Maiduguri, Ebere
Shekaru 5 ina sayarwa mutane mushen kaji a Maiduguri, Ebere
Source: Facebook

KU KARANTA: Sama da mutane 1500 sun kamu cutar Coronavirus ranar Alhamis

Shekaru 5 ina sayarwa mutane mushen kaji a Maiduguri, Ebere
Shekaru 5 ina sayarwa mutane mushen kaji a Maiduguri, Ebere
Source: Facebook

KU KARANTA: Miyetti Allah sun taimakawa Jami’an tsaro wajen ceto mutane 77 da aka yi garkuwa da su

Shekaru 5 ina sayarwa mutane mushen kaji a Maiduguri, Ebere
Shekaru 5 ina sayarwa mutane mushen kaji a Maiduguri, Ebere
Source: Facebook

A wani labarin kuwa, hukumar hana fasa kwauri ta kasa wacce aka fi sani da Kwastam ta sanar da kama alburusai da wasu haramtattun kaya da kudinsu ya kama Naira miliyan dari uku da saba'in da takwas da dubu dari bakwai da hamsin da daya da dari tara da talatin da biyar (N378,751,35.00).

Reshen hukumar na Owerri ne ya sanar da cewa ya kama alburusan da sauran kayan a tsakanin watan Nuwamba zuwa Disamba na shekarar 2020, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel