Kwastam ta gano alburusai 5,200 da aka boye cikin wasu kaya, kudinsu ya haura N378m

Kwastam ta gano alburusai 5,200 da aka boye cikin wasu kaya, kudinsu ya haura N378m

- Hukumar kwastam ta sake kama wasu alburusai da yawansu ya kai dubu biyar da dari biyu a boye a cikin wasu kayan amfani

- Shugaban ofishin hukumar kwastam da ke Owerri a jihar Imo, Yusuf Lawal, ya koka akan yawaitar safarar makamai zuwa Nigeria

- Ya lissafa wasu manyan kamun makamai da hukumar kwastam ta yi a sassan Nigeria a 'yan shekarun baya bayan nan

Hukumar hana fasa kwauri ta kasa wacce aka fi sani da Kwastam ta sanar da kama alburusai da wasu haramtattun kaya da kudinsu ya kama Naira miliyan dari uku da saba'in da takwas da dubu dari bakwai da hamsin da daya da dari tara da talatin da biyar (N378,751,35.00).

Reshen hukumar na Owerri ne ya sanar da cewa ya kama alburusan da sauran kayan a tsakanin watan Nuwamba zuwa Disamba na shekarar 2020, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Yayin da yake sanar da hakan, shugaban ofishin yankin, Kwantirola Yusuf Lawal Psc(+), ya bayyana damuwarsa akan yawaitar safarar makamai.

KARANTA: Ina kisa ne domin kawai na samu kudin shan giya da shagwaba budurwata - Matashi Tajudeen

Ya bayar da misalin yadda aka kama dumbin makamai a Lagos a shekarar 2017, a Kwara a shekarar 2018, da kuma baya bayan nan a Jihar Kebbi.

Kwastam ta kama alburusai da haramtattun kaya na fiye da N378m
Kwastam ta kama alburusai da haramtattun kaya na fiye da N378m Hoto: @Vanguard
Asali: Twitter

Ya kara da cewa duk da haka, sai gashi an sake kama wata mota da ke dauke da alburusai 5,200 a ranar 13 ga watan Disamba na shekarar 2020.

KARANTA: Wata daban: Daliban BUK sun ce basu shirya komawa makaranta ba tukunna, sun bayyana dalilansu

A cewar Lawal, an kama motar ne a hanyar Nwezenyi zuwa Ikom ta jihar Kuros Riba bayan samun sahihan bayanan sirri akan yadda aka boye alburusan a cikin sauran wasu kayan amfanin gida.

"Allah ne kadai yasan abinda zai faru da wadannan alburusai sun kai wurin da aka yi niyya, musamman yadda ake fama da matsalar garkuwa da mutane da fashi da makami da matsalar 'yan bindiga," a cewarsa.

A wani labarin, Legit.ng Hausa ta rawaito cewa fadar shugaban kasa ta yi raddi tare da yi wa jam'iyyar adawa ta PDP kaca-kaca.

A wani jawabi da Garba Shehu, kakakin shugaban kasa, ya fitar, fadar shugaba kasa ta ce duk wani sauran tasiri da PDP keda shi ya kare saboda ta zama jami'ar karya, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

A cewar fafa shugaban kasa, jam'iyyar PDP ba ta yi komai ba a tsawon mulkinta na shekaru goma sha shidda bayan assasa cin hanci da rashawa.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng