Miyetti Allah sun taimakawa Jami’an tsaro wajen ceto mutane 77 da aka yi garkuwa da su

Miyetti Allah sun taimakawa Jami’an tsaro wajen ceto mutane 77 da aka yi garkuwa da su

- Gwamnatin Katsina tace ana cigaba da fito da wadanda aka yi garkuwa da su

- Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association ce ta ke taka rawar gani

- Tun daga lokacin da aka fito da Yaran GSSS Kankara, ake ceto wasu mutanen

A ranar Alhamis, 7 ga watan Junairu, 2020, jami’an tsaro suka mikawa gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari wasu mutane da aka ceto.

Jaridar Punch tace jami’an tsaron sun yi nasarar kubuto da wadannan mutane har su 77 ne daga hannun ‘yan bindiga da su kayi garkuwa da su.

Mai girma gwamnan Katsina, Aminu Masari ya shaida cewa an ceto wadannan mutane ne a sakamakon hadin-gwiwar da jami’an tsaro suka yi.

Rt. Hon. Aminu Masari ya ce an samu hadin-kan sojojin kasa da na sama, jami’an DSS, ‘yan sanda da kuma kungiyar Makiyaya nan ta Miyetti Allah.

KU KARANTA: ‘Boko Haram’ sun sace Hakimi a harin da suka kai a Yobe

Gwamna Masari ya fadawa ‘yan jarida mutum 104 ke nan aka ceto a irin wannan shiri a Katsina.

Daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su, gwamnan ya ce 16 sun fito ne daga yankin Sabuwa, Faskari, Dandume, 10 kuma daga shiyyar Danmusa.

Ragowar wadannan mutane 77 da aka ceto kuma aka mika masa su ga gwamna a ranar Alhamis, sun fito ne daga kananan hukumomin Batsari da Jibia.

Gwamnan na Katsina yace ana cigaba da fito da wadanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su tun bayan da aka gano yaran makarantar nan da aka sace.

KU KARANTA: Daga ketare 'Yan bindiga su ka fito - Gwamna Bello

Miyetti Allah sun taimakawa Jami’an tsaro wajen ceto mutane 77 da aka yi garkuwa da su
Daliban GSSS Kankara da aka ceto Hoto; Twitter Daga: twitter.com/BashirAhmaad
Source: Twitter

“Mun gano wata hanya, kuma muna aiki da shugabannin Miyetti Allah da jami’an tsaro na ganin an ceto duk mutanen da zamu iya.” Inji Aminu Masari.

Kun ji labari cewa ana zargin ‘yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun shiga wani kauye, sun arce da Dattijon Basarake, wannan ya faru ne a cikin Jihar Yobe.

Iyalin Mai martaban sun shiga mawuyacin hali, sun roki gwamnati ta ceto ran wannan Hakimi.

Bayan haka, ‘yan ta’addan sun kona wasu daga cikin shagunan da ke garin. Wannan ya sa gwamna Mai Mala Buni ya ba SEMA umarni su kai agaji.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel