'Yan majalisa na duba yiwuwar hallarta noman wiwi a Najeriya

'Yan majalisa na duba yiwuwar hallarta noman wiwi a Najeriya

- Yan majalisar tarayya na yunkurin sahale amfani da wiwi kuma tuni kudirin ya tsallake karatun farko

- Za a sahale nomawa tare da kasuwancin wiwin don amfanin magani da bincike na kimiyya da lafiya

- Akwai tarin ka'idojin da ke tafe da dokar da kuma hukunce hukunce da aka tanada ga duka wanda ya saba dokar

'Yan majalisar wakilai na tarayya na yunkurin sahale dokar da zata halasta nomawa tare da kasuwancin wiwi don magani, kayan kwalliya, bincike da kuma samar da kudaden shiga ga Najeriya, The Punch ta ruwaito.

Wannan na zuwa ne a wani da kudiri na daidaita amfani da wiwi da Miriam Onuocho, ta gabatar a 2020, wanda ke jiran karatu na biyu a majalisar.

'Yan majalisa na duba yiwuwar hallarta noman wiwi a Najeriya
'Yan majalisa na duba yiwuwar hallarta noman wiwi a Najeriya. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan majalisar Ghana sun bawa hammata iska kan batun rinjaye (Bidiyo)

Anyi wa kudirin taken, 'dokar daidaita nomawa, mallaka, samarwa da kuma kasuwancin Wiwi don amfanin magani da bincike, da abubuwa masu alaka da haka'.

Noman wiwi da siyar da ita a Najeriya yanzu haka dai ya sabawa doka.

Idan kudirin ya zama doka, za a sahalewa asibitoci da likitoci rubuta wiwi a matsayin magani, sannan za a bar shagunan siyar da magani su dinga siyar da ita.

Sai dai dokar ta kunshi sharudan da ka'idojin nomawa, siye, siyarwa da kuma shan wiwin.

KU KARANTA: Tallafin Covid 19: 'Yan kasar Ghana za su sha wutar lantarki kyauta na watanni uku

Onuoha ta ce daga cikin dalilan kudirin akwai samar da "daidaita noma, mallaka, sarrafawa, samarwa tare da kasuwancin wiwi don magani da abin da ya shafi binciken".

Kadan daga cikin abin da kudirin ya kunsa, "mutumin da ke noma wiwi, safara ko siyarwa ba don amfanin magani ba kuma bai gabatar da takardun shaidar da ake da bukata ba, karkashin sashe na 12(1) ya aikata laifi kuma ana iya yanke masa hukuncin gidan yarin shekara biyu ko tarar da bata gaza miliyan daya ba ko kuma duka."

"Duk wanda aka sahalewa siyarwar kuma ya siyar ba bisa ka'ida ba, ya na cikin hadarin yin gidan yarin shekara biyu ko tarar N500,000 ko duka, shi kuma mai siyan da ya busa hayakin Wiwin ko yayi amfani da ita ba bisa ka'ida ba, za a iya yanke masa hukuncin shekara biyu a gidan yari ko ayi masa tarar da bata yi kasa da N500,000 ba ko duka biyun."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel