Tallafin Covid 19: 'Yan kasar Ghana za su sha wutar lantarki kyauta na watanni uku

Tallafin Covid 19: 'Yan kasar Ghana za su sha wutar lantarki kyauta na watanni uku

- Al'ummar kasar Ghana za su mori lantarki kyauta na tsawon watanni uku

- Gwamnatin kasar ne ta bada wannan umurnin a matsayin tallafin rage radadin korona

- Sanarwar ta ce mutane masu karamin karfe da ke amfani da kilowat 0 - 50 na za su amfana

Gwamnatin ƙasar Ghana za ta bayar da wutan lantarki na watanni uku kyauta masu ƙaramin ƙarfi a kasar tun daga watan Janairu zuwa Maris.

Rukunin waɗannan mutanen su ne waɗanda ba su amfani da wuta sosai akasin waɗanda ke da layukan wuta da yawa.

A cikin sanarwar ta suka fitar ranar Talata, Kwame Agyeman-Budu, shugaban kamfanin lantarki na Ghana ya ce wannan karamcin na cikin tallafin annobar korona ne da gwamnatin kasar ta bada.

Tallafin Covid 19: Yan Ghana za su sha wutan lantarki na watanni biyu kyauta
Tallafin Covid 19: Yan Ghana za su sha wutan lantarki na watanni biyu kyauta. @thecableng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hukumar yaki da rashawa ta Kano ta gano almundahana a hukumar bada tallafin karatu

Ya ce a ƙarƙashin shirin za a biya wa mutanen masu ƙaramin ƙarfi kudin wutansu na watanni uku daga watan Janairu zuwa Maris.

"Bisa umurnin shugaban kasar Ghana na kara wa'addin tallafin lantarki ga 'yan Ghana, gwamnatin Ghana (GG) zata cigaba da daukan dawainiyar biyan kudin lantarki na (kwastomomin da ke amfani da kilowat 0-50) na tsawon watanni uku daga Janairu zuwa Maris din 2021," a cewar Agyeman-Budu.

Sanarwar ta ce wadanda suka cika ka'idojin a biyu musu da ke amfani da mita za a saka musu lantarkin a cikin mitansu na watannin Janairu, Fabrairu da Maris.

KU KARANTA: Zaben kananan hukumomi: 'Yan takara 6 sun fadi gwajin miyagun kwayoyi a Kano

Wadanda kuma ba su amfani da mita ta zamani za su saka katinsu a cikin mita kafin su tafi ofishin hukumar domin a saka musu unit din lantarkin a ciki a kowanne wata.

Har wa yau, hukumar ta tabbatarwa dukkan kwastomominsu da masu ruwa da tsaki cewa za ta zartar da dukkan umurnin da gwamnatin kasar ta bada. Ta shawarci duk masu wata matsala su ziyarci ofishin yankinsu don a warware musu.

A wani labari na daban, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta bankado ayyukan almundahana a tallafin karatun kasashen waje na gwamnatin jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban hukumar, Magaji Rimingado, wanda ya bayyana haka ga yan jarida ranar Talata, ya ce daga 2015 zuwa 4 ga Janairun 2021, gwamnatin jihar ta kashe naira biliyan 7 a tsarin wanda ta gada daga gwamnatin da ta gabata, amma ana samun korafin daliban da suka rage a kasashen waje.

Ganin yadda korafe korafe suka yi yawa kuma ya kamata ace da yawa yawancin daliban sun kammala karatun su, gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya umarci hukumar da tayi "bibiya", bincika ta kuma dauki mataki akan badakalar", in ji Rimingado.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164