Tsohon shugaban Kano Pillars, Hamza, ya rasu yana da shekaru 70 a duniya

Tsohon shugaban Kano Pillars, Hamza, ya rasu yana da shekaru 70 a duniya

- Kungiyar Kano Pillars ta yi ta'aziyyar rasuwar tsohon shugabanta, Ɗanlami Hamza

- Marigayin ya rasu ne a ranar Lahadi bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a Kano

- Anyi jana'izar Hamza a maƙabartar musulmi da Abbatoir a Fagge a birnin Kano

Kano Pillars, a ranar Litinin, ta sanar da rasuwar tsohon shugaban kungiyar, Danlami Hamza.

Ya rasu ne a ranar Lahadi bayan fama da gajeruwar rashin lafiya, The Punch ta ruwaito.

Anyi jana'izar Hamza, wadda shine shugaban Pillars daga 1994 zuwa 1995 a maƙabartar Abbatoir da ke Fagge da taimakon ma'aikatan lafiya sanye da kayan kare kansu wato PPE.

Tsohon shugaban Kano Pillars, Hamza, ya rasu yana da shekaru 70
Tsohon shugaban Kano Pillars, Hamza, ya rasu yana da shekaru 70. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Dan majalisa zai bawa 'yan mazabarsa tallafin zomo a matsayin jari (Hoto)

Shugabannin kungiyar ƙarƙashin jagorancin Surajo Jambul cikin sanarwar da ta fitar ta shafin intanet na kungiyar ta nuna kaɗuwa bisa rasuwar tsohon shugaban kungiyar kuma ɗan majalisa.

Surajo ya bayyana tsohon shugaban kungiyar, wadda ya wakilci mutanen Fagge a matsayin mutumin da ya sadaukar da rayuwarsa don ginin kasa.

KU KARANTA: Shehu Sani ya shawarci matasan Arewa su kyale Kukah su mayar da hankali kan 'yan bindiga

Shugaban, a madadin yan wasa, masu bada horo, da mahukunta da magoya bayan kungiyar sun mika ta'aziyyarsu ga iyalan mamacin da Gwamna Dakta Abdullahi Ganduje.

A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, ministan tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, ya bukaci kiristoci da su yiwa kasa addu'ar zaman lafiya lokacin bukukuwan zagayowar haihuwar Almasihu wato kirsimeti.

Janar Magashi ya mika rokon a sakon taya kiristoci murnar Kirsimeti da ya fitar ranar Alhamis 24 ga watan Disamba kamar yadda Channels Tv ta ruwaito. Kirstimeti: Ku yi wa sojoji addu'a don kawo karshen tashin tsaro, Ministan tsaro.

Ya bukaci kiristoci da su zama kamar Yesu yayin bikin haihuwar tasa ta hanyar kyautatawa yan uwansu yan Najeriya ba tare da la'akari da bambancin addini ba sannan su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel