Dan majalisa zai bawa 'yan mazabarsa tallafin zomo a matsayin jari (Hoto)

Dan majalisa zai bawa 'yan mazabarsa tallafin zomo a matsayin jari (Hoto)

- Wani dan majalisa Tunji Ajuloopin zai rabawa al'ummar da yake wakilta zomo don samar sana'a da rage taulauci da zaman banza

-Dan majalisar mai wakiltar Ekiti/Isin/Irepodun/Oke-ero a majalisar wakilan tarayya ya kulla yarjejeniya da kungiyar masu kiwon zomo don tallafawa matasa

- Shugaban kungiyar masu kiwon zomon ya bayyana irin muhimmancin zomo da kuma irin ribar da ake samu, har ya kara da cewa matasa zasu rage wa iyaye wahala da dama

Tunji Ajuloopin, dan majalisa mai wakiltar Ekiti/Isin/Irepodun/Oke-ero a majalisar wakilan tarayya daga Jihar Kwara ya kulla yarjejeniya da kungiyar masu kiwon Zomo, RFA, a wani yunkurin tallafawa marasa aikin yi a al'ummar da yake wakilta.

Mista Ajuloopin yayin da ya ke karbar wakilcin kungiyar a ofishin mazaba ranar Litinin a Omu-Aran ya ce abin zai zama hanyar samar da sana'a ga matasa marasa aikin yi a yankin.

Da majalisa zai bawa 'yan mazabarsa tallafin zomo (Hoto)
Da majalisa zai bawa 'yan mazabarsa tallafin zomo (Hoto). Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe shugaban 'yan sintiri, sun sace mutane 8 a Katsina

"Ina so nayi wannan don samarwa da al'ummata aikin yi, da yawa daga ciki basu da aikin yi kuma za su gwada wannan, zai taimaka musu kwarai don saukaka rayuwa.

"Zamu kulla yarjejeniya da ku kuma zamu raba wanda zasu ci gajiyar zuwa rukuni rukuni, za ku ba su horo za kuma mu fara da karamin jari," a cewar sa.

Abdulrahman Femi, shugaban kungiyar RFA ya bayyana cewa dalibai a yankin na iya fara kiwon zomo don su tallafawa iyayen su, ya kara da cewa cikin shekara daya ko biyu zasu iya biyawa kansu.

A cewar sa, daliban yankin na iya dogaro da kiwon zomo don tallafawa iyayensu wajen biyan kudin makaranta, muna da nau'i daban daban wanda a dan kankanin lokaci za su iya kaiwa nauyin kilo 3.5 kuma a siyar a kasuwa.

KU KARANTA: Hattara: Yadda za a iya 'sace' bayanan katin ATM din ka

Mista Femi ya ce fitsarin zomo da kashin sa na da matukar amfani ga manoma, ya kara da cewa za a iya amfani da fitsarin a matsayin maganin kwarin gayayyaki.

Ya ce akwai masu bukatar zomo a kasuwanni a kasar nan, ya kuma ce ana bukatar shi sosai musamman mutanen da basa cin jan nama.

Ya kuma bayyana irin amfanin zomo ga lafiyar bil adama.

Kungiyar RFA din ta nada Mista Ajuloopin a matsayin uban kungiya a yankin Omu-Aran, lokacin da suke mika masa zomaye iri daban daban.

A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, ministan tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, ya bukaci kiristoci da su yiwa kasa addu'ar zaman lafiya lokacin bukukuwan zagayowar haihuwar Almasihu wato kirsimeti.

Janar Magashi ya mika rokon a sakon taya kiristoci murnar Kirsimeti da ya fitar ranar Alhamis 24 ga watan Disamba kamar yadda Channels Tv ta ruwaito. Kirstimeti: Ku yi wa sojoji addu'a don kawo karshen tashin tsaro, Ministan tsaro.

Ya bukaci kiristoci da su zama kamar Yesu yayin bikin haihuwar tasa ta hanyar kyautatawa yan uwansu yan Najeriya ba tare da la'akari da bambancin addini ba sannan su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: