2023: Shugabancin Igbo zai karfafa Nigeria, in ji tsohon gwamnan Bauchi

2023: Shugabancin Igbo zai karfafa Nigeria, in ji tsohon gwamnan Bauchi

- Isa Yuguda ya shiga sahun yan arewa da ke goyon bayan mika wa yankin kudu maso gabas shugabancin kasar a 2023

- Yaguda ya ce yin hakan zai kara karfafa hadin kan yankunan kasar a matsayin tsintsiya madaurinki daya

- Tsohon gwamnan ya ce shi ya yarda da adalci da daidaito a tsakanin yan kasar

Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Isa Yuguda, ya kasance daya daga cikin yan tsirarrun yan arewa da ke goyon bayan shugabancin Igbo gabannin zaben 2023.

A wata hira da jaridar The Sun a ranar Lahadi, 20 ga watan Disamba, Yuguda ya bayyana cewa idan aka baiwa yankin kudu maso gabas damar samar da shugaban kasar Najeriya na gaba a 2023, zai yi aiki sosai wajen hadin kan kasar.

Tsohon gwamnan na arewa ya bayyana cewa idan aka bai wa arewa da kudu maso yamma damar neman kujerar shugaban kada, zai kasance mai ma’ana ne kawai sannan ta bangaren hadin kan kasa shine ba dan Igbo damar hawa kujerar.

2023: Shugabancin Igbo zai karfafa Nigeria, in ji tsohon gwamnan Bauchi
2023: Shugabancin Igbo zai karfafa Nigeria, in ji tsohon gwamnan Bauchi Hoto: The Guardian
Source: UGC

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya ce zai mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu, 2023

Ya ce:

“Na yarda da adalci da daidaito da kuma kasarmu a matsayin tsintsiya daya. Tunda dai siyasa wasa ne, ya zama dole mu jajirce wajen gina amana a tsakanin yankunanmu wato arewa, gabas da yamma.

“Ya kamata a baiwa gabas damar shugabanci, amma kada a dauki hakan a matsayin yanci, illa dai a matsayin kwanciyar hankalin yan uwanmu, cewa a matsayinsu na yanki, suma sun riki matsayin.

“Idan arewa-kudu na tashi a yanzu, me zai hana arewa-yamma da gabas tashi? Idan wannan zai karfafa hadin kanmu da imani a kasarmu, mai zai hana mu samun shi? Shugabancin Igbo zai karfafa kasarmu.”

KU KARANTA KUMA: Yan Boko Haram sun yi garkuwa da fasinjoji 35 a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri

A wani labarin, Farfesa Usman Yusuf, wani shahararren jigon arewa, ya yi hasashe game da zaben Najeriya na gaba.

A wata hira da jaridar The Sun, Yusuf, wanda ya kasance tsohon sakatare na hukumar inshoran lafiya ta kasa (NHIS), ya ce yan siyasan da ke shirye-shirye don zaben 2023 suna rayuwa ne na muradin karya.

Legit.ng ta tattaro cewa jigon na arewa ya jadadda cewa zaben 2023 ba zai taba yiwuwa ba, musamman a arewa, duba ga matakin rashin tsaro a kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel