Shugaba Buhari ya ce zai mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu, 2023

Shugaba Buhari ya ce zai mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu, 2023

- Daga karshe Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya magantu a kan rade-radin da ke ikirarin cewa yana shirin makalkale mulki

- Shugaban kasar Najeriyan ya bayyana dalilin da yasa yake ziyartan mahaifarsa a jihar Katsina lokaci zuwa lokaci

- Buhari ya bayyana cewa akwai wata makarkashiya a satar dalibai a Kankara

Wani rahoto da ke billowa ya nuna cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya shirin ci gaba da kasancewa a kan mulki fiye da wa’adin da kundin tsarin mulkin Najeriya ta gindaya.

Shugaban kasar ya bayyana cewa zai mika mulki ga gwamnati na gaba a ranar 29 ga watan Mayun 2023, PM News ta ruwaito.

Ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, 18 ga watan Disamba, lokacin da yake jawabi ga daliban makarantar Kankara da wakilan iyayensu a dakin taro da ke gidan gwamnatin jihar Katsina.

Shugaba Buhari ya ce zai mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu, 2023
Shugaba Buhari ya ce zai mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu, 2023 Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

KU KAARANTA KUMA: Yan Boko Haram sun yi garkuwa da fasinjoji 35 a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri

Buhari ya ce:

“Na kan ziyarci mahaifata saboda nayi rantsuwa da Qur’ani mai tsarki cewa zan kare kundin tsarin mulkin kasar, don haka dole na mika mulki ga gwamnati na gaba a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

“Saboda haka, idan Allah ya sani cikin rayayyu, shakka babu zan zo gida. Wannan ne yasa nake ziyartan gida.”

Shugaban kasar ya kuma yi ikirarin cewa sace wasu dalibai da aka yi daga wata makarantar gwamnati a Kankara, jihar Katsina shiri ne na da gangan don tozarta gwamnatinsa.

A cewar jaridar Vanguard, ya ce ba kicibis aka samu ba sace yaran a ranar da ya ziyari mahaifarsa, Daura.

KU KARANTA KUMA: Maina: Irin rayuwar da nayi a kurkuku tsawon kwanaki 5, Ndume

A wani labarin, Farfesa Usman Yusuf, wani shahararren jigon arewa, ya yi hasashe game da zaben Najeriya na gaba.

A wata hira da jaridar The Sun, Yusuf, wanda ya kasance tsohon sakatare na hukumar inshoran lafiya ta kasa (NHIS), ya ce yan siyasan da ke shirye-shirye don zaben 2023 suna rayuwa ne na muradin karya.

Legit.ng ta tattaro cewa jigon na arewa ya jadadda cewa zaben 2023 ba zai taba yiwuwa ba, musamman a arewa, duba ga matakin rashin tsaro a kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel