Matata tana kwanciya da makabci na, mijin da ya nemi kotu ta raba auren sa ya bayyana

Matata tana kwanciya da makabci na, mijin da ya nemi kotu ta raba auren sa ya bayyana

- Kotu ta raba auren shekara 21 a bisa cin amanar aure bayan da mijin ya bukaci hakan a kotun gargajiya ta Mapo a Ibadan

- Hamzat yayi ikirarin cewa matar tasa tana kwanciya da wani makwabcin sa zargin da Mujidat din ta karyata

- Kotu ta raba auren kuma ta raba yayan su biyar, inda manyan su uku aka baiwa mijin biyu kuma matar

Wani direban tasi, Kazeem Hamzat, ya bayyanawa kotun gargajiya ta Mapo a Ibadan, da ta raba auren shekara 21 tsakanin sa da matarsa, Mujidat bisa zargin cin amanar aure, Daily Nigerian ta ruwaito.

Hamzat ya shaidawa alkalin kotun Ademola Odunade da sauran alkalan Alhaji Sulaiman Apanpa da kuma Alhaji Rafiu Raji cewa rayuwar sa ta na cikin hadari matukar ya ci gaba da zama da Mujidat.

Matata tana kwanciya da makabci na, mijin da ya nemi kotu ta raba auren sa ya bayyana
Matata tana kwanciya da makabci na, mijin da ya nemi kotu ta raba auren sa ya bayyana. Hoto: @Vanguardngr
Source: Twitter

Da ya ke jawabi, mutumin mai yaya biyar da yake zaune a Odo Oba da ke Ibadan, ya ce ya sha kama Mujidat a wani irin yanayi da wani makwabcinsa da wasu mazan ma daban.

"Wata rana bazan manta ba, na dawo daga aiki sai Mujidat take cewa ya kamata mu nemi wani ɗakin haya don karawa akan wanda muke dashi.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe Kanawa 16 a titin Kaduna zuwa Abuja

"Na nuna rashin amincewa akan dalilin da ta bani, amma a haka na yarda saboda ban san bukatar ta ba.

Bayan yan kwanaki, na tashi tsakar dare saboda sautin muryar wata mata a kusa da gidan mu, kuma na yanke shawarar duba me yake faruwa.

"Na duba sabon dakin in da matar ta wa take kwana, amma sai na ga bata nan.

"Sai na lura muryar na fitowa daga dakin wani gwauro da ke makwabtaka da mu, kuma na buga kofa fiye da awa daya ba wanda ya bude.

"Sauran makwabta ne suka ce in hakura in barwa Allah.

"Hakan ta ci gaba da faruwa kuma Mujidat ta ce min zan kashe kaina matukar na ci gaba da bibiyar harkokinta. "

Da take maida martani, Mujidat mai aikin share ta karyata zargin, ta kuma bayyana mutumin da mijin ta yake magana a matsayin wanda ba zai iya kwanciya da mace ba.

Da kotun ta bukaci karin bayani, Mujidat ta tabbatar da cewa ba shi da karfin kwanciya da mace saboda "mahaifiyar mutumin ta ce dan ta bashi da lafiya kuma ba zai iya kwanciya da mace ba.

KU KARANTA: Hatsarin mota ya halaka mutane 40 a Adamawa, FRSC

"Hamzat mugun mutum ne wanda bai taba yarda dani ba. Ya saka min "mugun" (wani maganin gargajiya na kama masu cin amanar aure) a wurare daban daban."

Da kotu take yanke hukunci, ta raba auren saboda kar abin ya kai ga babbar barna.

Daga cikin yaran su biyar an bawa Hamzat manyan su uku, ragowar biyu kuma aka baiwa Mujidat.

Haka kuma Hamzat zai dinga bawa Mujidat naira 6,000 a matsayin kudin ciyarwa kuma zai dauki nauyin karatun su.

A wani labarin, rundunar sojojin ruwan Najeriya ta fitar da wani sanawar dauke da hotuna da sunayen wasu jami'anta da suka tsere daga aiki tana mai neman duk wanda ke da bayani da zai taimaka a kamo su ya tuntubi ofishinta ko na 'yan sanda mafi kusa.

The Punch ta ruwaito cewa an wallafa sanarwar ne a hedkwatar rundunar sojin ruwan da ke binrin tarayya Abuja. Rundunar soji tana neman jami'anta 43 ruwa a jallo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel