Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka Soji 10, sun kwace sabon motar yaki

Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka Soji 10, sun kwace sabon motar yaki

Akalla Sojojin Najeriya 10 sun rasa rayukansu a harin da yan ta'addan ISWAP suka kai musu yankin Alagarno-Timbuktu dake jihar Borno, Arewa maso gabashin Najeriya.

A cewar AFP, bisa rahoton da ta samu, an kashe Sojojin 10 ne bayan harin kwanton baunan da aka kaiwa Sojojin ranan Litinin a Alagarno.

"Mun yi rashin Sojoji 10 a fada kuma yan ta'addan sun dauke daya," majiyar ta bayyana.

A cewar wata majiyar kuwa, "An yi mumunan artabu kuma an kashe yan bindigan, amma sun galabe Sojojin."

HumAngle ta ruwaito cewa Sojojin sun tafi sintiri ne yayinda suka yi arangama da yan ta'addan ISWAP a hanya.

An kwace manyan motocin yakin Sojojin Najeriya.

Yan ta'addan sun kwace mota kirar Toyota Buffalo da sabuwar motar yaki KIA KLTV-181 da kamfanin Kia Motors ta kera.

An tattaro cewa yan watanni da suka gabata aka kaddamar da motar yakin kuma an ruwaito cewa tana da matsaloli musamman wajen amfani da ita a filin daga.

KU DUBA: Ba zamu sake lamuntan kisan yan Arewa a kudu ba, Kungiyar dattawan Arewa

Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka Soji 10, sun kwace sabon motar yaki
Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka Soji 10, sun kwace sabon motar yaki Credit: @HumAngle
Source: Twitter

KU KARANTA: Lanbo ko ciwo: Jerin manyan da su ka zama marasa lafiyan dole a zauren shari’a

Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka Soji 10, sun kwace sabon motar yaki
Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka Soji 10, sun kwace sabon motar yaki Hoto: KIA/HLTV
Source: Twitter

A wani labarin daban, sojojin da aka tura yaki da yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya, sun koka kan yadda aka manta da su a wajen babu hutu shekaru biyar yanzu.

HumAngle ta samu bayani daga jaruman Sojojin 3 Bataliya dake Gamboru/Ngala cewa an tura su yaki da yan Boko Haram tun ranar 28 ga Febrairun 2016.

"Wannan ne shekaran mu na biyar muna yaki a filin daga kuma ba'a canza mu ba. Wasu Sojojin da aka kawo mu tare sun samu sauyi," daya daga cikin Sojojin da aka sakaye sunansa ya bayyana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel