Gaskiya mun gaji: Sojojin dake yaki da Boko Haram tun 2016 a Borno sun koka

Gaskiya mun gaji: Sojojin dake yaki da Boko Haram tun 2016 a Borno sun koka

Sojojin da aka tura yaki da yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya, sun koka kan yadda aka manta da su a wajen babu hutu shekaru biyar yanzu.

HumAngle ta samu bayani daga jaruman Sojojin 3 Bataliya dake Gamboru/Ngala cewa an tura su yaki da yan Boko Haram tun ranar 28 ga Febrairun 2016.

"Wannan ne shekaran mu na biyar muna yaki a filin daga kuma ba'a canza mu ba. Wasu Sojojin da aka kawo mu tare sun samu sauyi," daya daga cikin Sojojin da aka sakaye sunansa ya bayyana.

Ya ce sun dade suna kuka ga Kwamandoji da manyan jami'an dake kawo musu ziyara amma abin ya ci tura.

"An canza dukkan hafsoshin da muka zo tare. Har da wadanda suka same mu a nan an canza su. Shin ba jini daya ke yawo cikin jikinmu ba?", Sojan ya kara.

"Ba sa tunanin halin da muke ciki da na iyalanmu,"

"Mu 3 Bataliya muna rokon babban hafsan Soji yayi wani abu."

"Bamu samun sauki a Rann da Gamboru Ngala. Mun gaji da wajen nan. Muna son komawa gida don ganin iyalanmu," Ya kara.

Ya yi kira ga gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya sa baki.

A cewar hafsan, hedkwatar Soji ta yi tsarin cewa duk Sojan da yayi sama da shekaru biyu da rabi a Arewa maso gabas zai samu sauyi.

Wani Hafsa a karamar hukumar Kala/Balge, ya bayyanawa wakilin HumAngle, cewa tsawaita zamansu a wajen ya ruguza tsakanin mutane da yawa da iyalansu.

Gaskiya mun gaji: Sojojin dake yaki da Boko Haram tun 2016 a Borno sun koka
Gaskiya mun gaji: Sojojin dake yaki da Boko Haram tun 2016 a Borno sun koka Credit: HumAngle
Source: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel