Ba zamu sake lamuntan kisan yan Arewa a kudu ba, Kungiyar dattawan Arewa

Ba zamu sake lamuntan kisan yan Arewa a kudu ba, Kungiyar dattawan Arewa

- Dattawan Arewa sun yi tattaki har kudu domin tattaunawa da gwamnonin yankin

- Dattawan sun yi alhinin yadda ake kaiwa yan arewa mazauna kudu hari lokacin zanga-zangan EndSARS

- An kona Masallatai a jihar Abiya da Enugu kuma an yi asarar dukiyoyin yan Arewa

Kungiyar dattawan Arewa a ranar Talata ta alanta cewa ba za ta sake lamuntan harin da ake kaiwa mutan Arewa dake zama a kudancin Najeriya ba.

Shugaban kungiyar, Farfesa Ango Abdulahi ya bayyana hakan a garin Fatakwal inda suka gana da al'ummar Arewa dake zama a jihar Rivers, rahoton Punch.

Yayinda ya bayyana cewa sun zo jihar domin jajantawa 'yan uwansu da aka kai wa hare-hare yayin zanga-zangar EndSARS, ya ce abin ya bayyana karara wasu yan yankin Inyamurai (kudu maso gabas) ke kashe yan Arewa.

"Abinda ke bamu mamaki shine wadanda ke kai wadannan hare-hare kan yan Arewa su ne mutanen dake kuka kuma suke neman diyya," yace.

"Mun ji dadi lokacin da mukayi magana da gwamnan (Nyesom Wike) na jihar. Mutanen jihar sun fada mana cewa gwamnan musamman ya kare su."

"Abun ya fara bayyana yanzu cewa wadanda ke kaiwa yan Arewa hari a kudu mutanen kudu maso gabas ne."

"Ya zama wajibi gwamnatocin kudu su tabbatar mana da cewa wannan ba zai sake faruwa ba. Kuma ina ganin Arewa ba zata sake lamuntan haka ba."

KU KARANTA: Nana Akufo-Addo ya lashe zaben kasar Ghana

Ba zamu sake lamuntan kisan yan Arewa a kudu ba, Kungiyar dattawan Arewa
Ba zamu sake lamuntan kisan yan Arewa a kudu ba, Kungiyar dattawan Arewa Credit: @GovWike
Source: Twitter

DUBA NAN: Dr Isa Pantami ya yi umurnin dakatad da sayar da sabbin layukan waya

A bangare guda, gamayyar kungiyoyin Arewa a ranar Talata ta yi Alla-wadai da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari kan yadda rashin tsaro ya tabarbare a Arewacin Najeriya.

A jawabin da Kakakin gamayyar, Abdul-Azeez Sulaiman, ya saki, ya ce Arewacin Najeriya yanzu ta zama filin yaki saboda yan Boko Haram, masu garkuwa da mutane, barayin shanu da masu fyade, wadanda ke cin karkukansu ba babbaka.

Kungiyar ta tuhumi shugabannin Arewa da masu fada aji, da daukan abinda ke faruwa wasa saboda su da iyalansu na wurare masu lumana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel