Birbishin rikici tsakanin Sanata Ahmad Lawan da Gwamna Mai Mala Buni

Birbishin rikici tsakanin Sanata Ahmad Lawan da Gwamna Mai Mala Buni

- Yunkurin tsawaita wa'adin kwamitin gwamna Buni ka iya sabbaba rabuwan kai tsakanin 'yayan jam'iyyar

- Wasu Sanatoci da gwamnoni na son a tsawaita wa'adin

- Amma shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan da wasu sanatoci na adawa da hakan

Yayinda ake shirin zaman majalisar zartaswar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a yau, da alamun Sanata Ahmad Lawan na fuskantar tawaye daga wajen wasu Sanatoci.

The Sun ta ruwaito cewa yanzu haka kan Sanatoci APC a rabe yake a majalisar.

Yayinda masu goyon bayan Ahmad Lawan ke nuna rashin amincewarsu da tsawaita wa'adin kwamitin rikon kwaryan jam'iyyar karkashin gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, sauran adawa da shi na son a tsawaita.

Wani Sanatan APC da aka sakaye sunansa yace rikicin da ke tsakanin Sanata Ahmad Lawan da Gwamna Buni, kawai suna yi ne don zaben shugaban kasan 2023.

Ya ce Lawan da Buni na neman kujeran mataimakin shugaban kasa idan aka zabi dan kudu matsayin shugaba.

Ya ce masoyan Lawan dake yakin kujeran mataimakin shugaban kasa a 2023, na kokarin ganin cewa sun nada nasu matsayin shugaban jam'iyyar, saboda gwamnoni sun kwaceta.

"A baya, ana juyawa da yan majalisar dattawa a harkokin jam'iyyar...Amma a yau APC na harkokinta ba tare da tuntubar yan majalisa ba kuma hakan ba abu mai kyau bane yayinda ake durfafan 2023, " Sanata yace.

"Idan aka daina juyawa da Sanatoci, da yawa cikinsu zasu zama bayin gwamnoni kafin su samu tikiti a 2023. Kuma gaskiya rikicin dake tsakanin Lawan da Buni na tsananta lamarin."

"Su biyun na neman kujera daya...Su na son zama yan takaran mataimakin shugaban kasa ga duk wanda aka zaba daga kudu a 2023," Sanatan ya kara.

Daga baya an samu labarin cewa Sanatoci daga Arewa na hada kai da gwamnoninsu domin tsawaita wa'adin kwamitin Buni.

Yawancin wadanda basu son tsawaita wa'adin, an samu labarin cewa yan Kudu maso yamma da kudu maso kudu ne.

KU KARANTA: Bayan soyewa na shekaru 8 babu niyyar aure, budurwa ta maka saurayi a kotu

Birbishin rikici tsakanin Sanata Ahmad Lawan da Gwamna Mai Mala Buni
Birbishin rikici tsakanin Sanata Ahmad Lawan da Gwamna Mai Mala Buni Hotuna: @DrAhmadLawan @kfayemi
Asali: Twitter

KU DUBA: Gwamna Zulum ya kai ziyara Gwoza, ya rabawa mutane N24m da kayan hatsi ga mutane 1200

A bangare guda, wasu fusattun matasa a jihar Benuwe sun lalata gida da motocin shugaban jam'iyyar APC, Kwamared Abba Yaro, sakamakon mutuwar fuju'a da ɗaya daga cikin ma'aikatan gidansa yayi.

Jaridar Daily Trust ta tattara rahotannin yadda fusattun matasan suka fasa tagogin gidan, baya ga motoci da na'urorin sanyaya ɗakin gidan shugaban jam'iyyar.

Shaidu sun nuna cewa matasan sun fusata sakamakon dalilin da ya yi sanadiyyar mutuwar mai gadin Kwamared Abba Yaro.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel