Fusatattun matasa sun lalata gida da motar shugaban jam'iyyar APC na Benue bisa mutuwar ma'aikacin gidansa

Fusatattun matasa sun lalata gida da motar shugaban jam'iyyar APC na Benue bisa mutuwar ma'aikacin gidansa

- Fusatattun matasa sun lalata gida da motar shugaban jam'iyyar APC na jihar Benuwe, Kwamared Abba Yaro

- Matasan sun fusata ne sakamakon mutuwar fuju'a da ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan shugaban ya yi

Wasu fusattun matasa a jihar Benuwe sun lalata gida da motocin shugaban jam'iyyar APC, Kwamared Abba Yaro, sakamakon mutuwar fuju'a da ɗaya daga cikin ma'aikatan gidansa yayi.

Jaridar Daily Trust ta tattara rahotannin yadda fusattun matasan suka fasa tagogin gidan, baya ga motoci da na'urorin sanyaya ɗakin gidan shugaban jam'iyyar.

Shaidu sun nuna cewa matasan sun fusata sakamakon dalilin da ya yi sanadiyyar mutuwar mai gadin Kwamared Abba Yaro.

An samu bayanan cewa marigayin ya mutu ne sanadiyyar jan wuta a ƙoƙarin sare wani reshe da ya ke taɓa babbar wayar lantarkin da ta wuce ta saman gidan.

KARANTA: A villa ake iskanci na gaske kuma Buhari ne jagora; Aisha ta mayar da martani a kan gargadin shugaba Buhari

Wasu maƙwabtan wurin sun shaidawa manema labarai cewar an hangi gawar marigayin da safiyar ranar Litinin tana reto a jikin bishiyar, lamarin da ya harzuƙa matasan kenan.

Fusatattun matasa sun lalata gida da motar shugaban jam'iyyar APC na Benue bisa mutuwar ma'aikacin gidansa
Fusatattun matasa sun lalata gida da motar shugaban jam'iyyar APC na Benue bisa mutuwar ma'aikacin gidansa
Source: UGC

Amma shugaban jam'iyyar ya ƙaryata yadda abin baƙincikin ya faru, inda yace hayaniyar jama'a ce ta tashe shi daga barci, kuma da ya buƙaci ba'asi sai aka gaya masa cewa ɗaya daga cikin mai gadin gidan ne wutar lantarki ta ja shi lokacin sare reshen bishiyar da ya haɗu da babbar wayar lantarkin da ta bi ta saman gidan.

"Da na tambayi ɗaya mai gadin, ya faɗa min cewar sai da ya gargaɗi marigayin kan kada yayi gangancin hawa sare reshen bishiyar saboda ya taɓa wayar lantarki, amma sai ya ce dashi ya san yadda zai sare, daga nan wutar ta ja shi."

"Muna cikin tattauna yadda abun ya wakana ne, sai matasan suka zuge ƙofar gidan suka danno kai ciki suka lalata gidan, kamar yadda ka ke gani sun lalata ko'ina," a cewarsa.

KARANTA: Gwamnatin jihar Kaduna ta rushe gidaje 50 a kusa da cibiyar Idanu

Yaro, ya ce, ziyarar gaggawa da gwamna Samuel Ortom ya kawo min ita ce ta cece ni da iyalina daga barazanar harin matasan.

Gwamna Ortom wanda ya ziyarci wurin ya yi tirr da faruwar lamarin, inda ya shawarci fusattun matasan da su daina ɗaukar doka a hannunsu idan wani abu ya rikice.

Ya ce akwai buƙatar mutane suke barin hukumomin da abin ya shafa aiwatar da irin wannan ayyukan idan buƙatar hakan ta taso.

Legit.ng ta rawaito cewa ma'aikatan wucin gadi guda biyu da suka bace yayin zaben maye gurbi na ranar Asabar a jihar Zamfara sun bayyana, TheCable ta rawaito ranar Litinin.

An samu matsalar satar akwatin zabe da barkewar rikici a mazabar 001 da ke karamar hukumar Bakura yayin zaben maye gurbin.

Yayin da take gabatar da sakamakon mazabar, wakiliyar INEC mai kula da mazabar, A'isha Bawa, ta ce ta nemi ma'aikatan Sama ko kasa, ba ta gansu ba, sun bace bat bayan barkewar rikici.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel