Bayan soyewa na shekaru 8 babu niyyar aure, budurwa ta maka saurayi a kotu

Bayan soyewa na shekaru 8 babu niyyar aure, budurwa ta maka saurayi a kotu

- Wata mata ta maka saurayinta a kotu saboda ya ki mayar da hankali ya aureta duk da shekarunsu 8 a tare

- A cewarta har haifa masa da daya tayi, amma har yanzu shiru ya bayar da sadakinta amma ya ki aurenta

- Saurayin ya kare kansa, inda yace ba shi da isasshen kudin aurenta, sannan ba ta bashi cikakkiyar kulawa

Wata mata ta maka saurayinta a kotu sakamakon bata mata lokaci duk da shekarunsu 8 tare amma ya gaza aurenta.

Ngoma ta sanar da wata kotu a Zambia cewa ta gaji da jiran Herbert Salaliki mai shekaru 28, wanda yayi mata alkawarin aure.

A cewar Mwebantu, har yanzu Ngoma tana zaune da iyayenta duk da ta haifa wa Herbert da guda daya, shi kuma yana zaman kansa.

Kamar yadda aka samu rahotonni, saurayin ya biya sadakin budurwar amma har yanzu bai aureta ba.

Bayan soyewa na shekaru 8 babu niyyar aure, budurwa ta maka saurayi a kotu
Bayan soyewa na shekaru 8 babu niyyar aure, budurwa ta maka saurayi a kotu. Hoto daga www.mwebantu.com
Asali: UGC

KU KARANTA: NAAT ta bai wa FG shawara muhimmiya a kan karbar tsarin UTAS na malaman jami'a

Ngoma ta bayyana cewa ta gaji da jiransa, shiyasa ta maka shi a kotu sakamakon yi mata wasa da rayuwarta.

A cewarta: "Har yanzu ya ki mayar da hankali, shiyasa ta kawo kararsa a kotu saboda ya kamata a ce ta san inda ta dosa da rayuwarta."

Ngoma ta ce tana zarginsa da ha'intarta, bayan ta gano yana tura wa wata budurwa sako tana ganin wani abu yana faruwa tsakaninsu.

Herbert ya kare kansa, inda yace bashi da isassun kudaden da zai iya aurenta, sannan ya ce Ngoma bata bashi cikakkiyar kulawa.

Alkalin ya shawarcesu da suyi kokarin sasanta junansu, saboda har yanzu babu wata shaida ta aurensu.

KU KARANTA: Cike da farin ciki, jaruma Rahama Sadau ta wallafa hotuna yayin cikarta shekaru 27

A wani labari na daban, wani mutum mai karancin shekaru, Roy Jairus Watuulo ya rasu washegarin daurin aurensu. Mutumin dan Kampala, kasar Uganda, ya zama angon kyakkyawar matar kenan, ashe rayuwa ba za tayi tsawo ba.

An daura aurensa da Anita Nabaduwa a ranar Asabar, 5 ga watan Disamba, washegari ajalinsa ya riske shi.

Bayan an gama shagalin aurensa, ya fara fadin yana jin alamun ciwo. Sai aka garzaya dashi asibiti da tsakar dare ya rasu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng