Gwamna Zulum ya kai ziyara Gwoza, ya rabawa mutane N24m da kayan hatsi ga mutane 1200

Gwamna Zulum ya kai ziyara Gwoza, ya rabawa mutane N24m da kayan hatsi ga mutane 1200

- Bayan kwato garin daga hannun Boko Haram, mutane sun fara komawa rayuwarsu a Gwoza

- Gwamnan Borno ya ziyarci garuruwa uku a karamar hukumar da ta fuskanci kalubalen Boko Haram

- Ya ce za'a bude makarantu kuma a ci gaba da rayuwa a Gwoza

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, a ranar Litinin, ya raba milyan 24 ga mutane 1200 a tsohuwar hedkwatar yan ta'addan Boko Haram, Gwoza.

A jawabin da kakakin gwamnan, Mallam Isa Gusau, ya saki, ya ce maigidansa ya yi amfani da ranar Litinin wajen kai tallafi garin Ngoshe, Warabe da Pulka, a karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.

Jawabin ya ce gwamnan ya jagoranci rabon kayan abinci da kudi N24m ga mutane 1200 mabukata da suka dawo garin daga Pulka da Maiduguri.

An ruwaito gwamnan na cewa an yi rabon ne domin cigaba da taimakawa mutanen da suka dawo garin gabanin damina da zasu fara noma.

"Gwamnan ya yi amfani da wannan dama wajen duba wasu ayyuka, kuma bayan haka ya umurci cibiyar ilmin firamare ta yi gaggawar samar da kujeru da tabbatar da cewa an bude makarantar firamaren Ngoshe nan da makonni biyu, " jawabin yace.

Hakazalika gwamnan ya je Waraba a karamar hukumar Gwoza, inda ya duba gidaje 350 da ake ginawa mutanen da suka yi asaran gidajensu sakamakon rikicin Boko Haram.

Kalli hotunan:

Gwamna Zulum ya kai ziyara Gwoza, ya rabawa mutane N24m da kayan hatsi
Gwamna Zulum ya kai ziyara Gwoza, ya rabawa mutane N24m da kayan hatsi Credit: @GovBorno
Source: Twitter

KU DUBA: Gwamnatin jihar Kaduna ta rushe gidaje 50 a kusa da cibiyar Idanu

Gwamna Zulum ya kai ziyara Gwoza, ya rabawa mutane N24m da kayan hatsi
Gwamna Zulum ya kai ziyara Gwoza, ya rabawa mutane N24m da kayan hatsi Credit: @GovBorno
Source: Twitter

KU KARANTA: Fusatattun matasa sun lalata gida da motar shugaban jam'iyyar APC na Benue bisa mutuwar ma'aikacin gidansa

Gwamna Zulum ya kai ziyara Gwoza, ya rabawa mutane N24m da kayan hatsi
Gwamna Zulum ya kai ziyara Gwoza, ya rabawa mutane N24m da kayan hatsi Credit: @GovBorno
Source: Twitter

A bangare guda, yan Najeriya sun caccaki Zulum kan cewa da yayi tsaro ya inganta a Borno karkashin Buhari

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, a ranar Lahadi, 6 ga watan Disamba ya ce duk da kisan akalla manoman shinkafa 43 da mayakan Boko Haram suka yi kwanan nan, lamarin tsaro ya inganta a jihar karkashin gwamnatin Buhari.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a Maiduguri, babbar birnin jihar Borno lokacin da ya karbi bakuncin dattawan arewa karkashin jagorancin babban jigon kungiyar, Ambassador Shehu Malami, da Shugaban kungiyar, Audu Ogbeh.

yar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel