Paris Club: Shugaba Buhari ya bamu Naira Biliyan 47 inji Gwamnan Jigawa

Paris Club: Shugaba Buhari ya bamu Naira Biliyan 47 inji Gwamnan Jigawa

- Gwamnatin Tarayya ta ba Jihar Jigawa N47b da take binta bashi

- Gwamnan Jigawa, Badaru Abubakar ya tabbatar da wannan jiya

- Biliyan 10 daga cikin kudin sun fito ne daga aikin filin jirgin sama

Mai girma gwamnan Jigawa ya bayyana cewa jiharsa ta karbi wasu kudinta da ta ke jira daga hannun gwamnatin tarayyar Najeriya.

The Nation ta rahoto cewa Muhammadu Badaru Abubakar ya tabbatar da karbar fiye da Naira biliyan 47 daga hannun gwamnatin tarayya.

Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar yace an dawo masu da wannan kudi ne saboda abin da gwamnatin jiha ta kashe wajen gina filin jirgi.

Bayan haka akwai kudin bashin Paris Club wanda gwamnati ta karba da yanzu ya dawo hannun gwamnatin jihar Jigawa, jaridar ta rahoto haka.

KU KARANTA: An kai karar tsohon Gwamnan jihar Zamfara, Ahmad Sani Bakura gaban NHRC

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kakakin Majalisar Dokokin Wata Jiha a Najeriya Ya Rasu

Gwamnan ya yi wannan bayani ne a ranar Lahadi, 6 ga watan Nuwamba, 2020, wajen kaddamar da titin Balago zuwa Auno mai-cin kilomita 42.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Badaru Abubakar ya ce an ba jiharsa Naira biliyan 37 na bashin Paris Club da gwamnatin tarayya ta karba.

Bayan haka gwamnatin tarayya ta aiko wa jihar Naira biliyan 10 a matsayin abin da ta batar wajen gina filin jirgin sama na jihar Jigawa a Dutse.

Da yake na shi jawabin, shugaban gwamnonin APC, Atiku Bagudu, ya yabi gwamnan Jigawa.

KU KARANTA: Matsalar tsaro ta sa anyi wa Al-Kur’ani sauka rututu a Maiduguri

Paris Club: Shugaba Buhari ya bamu Naira Biliyan 47 inji Gwamnan Jigawa
Badaru Abubakar Hoto: www.pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Sanata Atiku Bagudu ya ce Badaru Abubakar ya ciri tuta wajen takatsan-tsan a kashe dukiyar al’umma.

Atiku Bagudu yake cewa titin da za a gina daga Balago zuwa Auno zai taimaka wa tattalin arzikin mutanen wannan yanki da sauran al’ummar yankin.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Peter Obi Ya Gana da Wani Gwamnan Arewa, Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Tinubu, Atiku da Kwankwaso

A baya kun ji yadda Boko Haram su ka yanka wani Bawan Allah wanda Matar shi ta haihu, ya je neman masu abinci a lokacin da aka kai hari a Zambari.

Bayan kwana 7 da harin Zabarmari, Mai Garin kauyen. ya fito ya bada labarin abubuwan da suka auku a lokacin da aka kawo masu hari a wata Asabar.

Sannan Mai Garin Zabarmari yace karya ne, ba su bukatar amincewar Sojoji kafin su shiga gonakinsu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng