Mai garin Zabarmari ya bayyana ainihin abubuwan da suka faru a harin Boko Haram

Mai garin Zabarmari ya bayyana ainihin abubuwan da suka faru a harin Boko Haram

- Manema labarai sun yi hira da Mai Garin Zabarmari bayan mugun abin da ya auku

- Alhaji Zanna Bukar Lawan ya bada labarin irin ta’adin da Boko Haram su kayi masu

- Mai Garin ya ce mafi yawan wadanda aka hallaka matasa ne masu kananun shekaru

Jaridar Punch tayi hira da Mai garin Zabarmari, Zanna Bukar, inda ‘yan ta’addan Boko Haram su ka hallaka mutane rututu a cikin ‘yan kwanakin nan.

Alhaji Zanna Lawan Bukar mai shekaru 53 ya bada labarin yadda suke zaman lafiya a da, harin da Boko Haram suka kawo masu, da irin ta’adin da aka yi.

Zanna Lawan Bukar yace a zamanin baya, su kan kai har dare a gonaki, akasin halin da ake ciki a yau, inda ‘yan ta’adda suke yi wa mutane yankan rago.

Da aka tambayi Mai garin game da zuwa gona ba tare da iznin sojoji, ba sai ya ce:

“Duk wanda ya yi wannan maganar ya jahilci halin da ake ciki a kauyen nan. Idan ka yi bincike a kan Zabarmari, za ka fahimci cewa mu na zaman lafiya duk da tashin hankalin da ake ciki.”

KU KARANTA: "Ina kallo aka yanka a 'ya 'ya na" - Mahaifi

Ya ce: “Ko da an yi lokacin da aka sace mana dabbobi, kona mana gonaki, aka kashe ‘yanuwanmu, amma ba a taba kai wa ga sai mun nemi iznin jami’an tsaro kafin mu je gona ba.”

Wannan dattijo ya shaida wa ‘yan jarida cewa mutanen kirki daga yankunan Zamfara, Katsina da Kebbi da kuma Bare-bari da Shuwa su ka cika wannan gari na su.

Zanna Bukar ya ce ba za su taba barin wani bata-gari ko bakin-ashana ya zauna tare da su ba.

Mai garin ya ce wajen karfe 11:00 na safe su ka samu labarin Boko Haram su na cafke manoma su na shiga da su kauyen Kwashebe.

Bayan wasu sun tsero ne su ka sanar da jama’a cewa an yanka wasu, kuma ‘yan Boko Haram sun sake su ne domin su bada labarin yankan ragon da su ka yi.

KU KARANTA: An gano wasu gawa a Zabarmari

Mai garin Zabarmari ya bayyana ainihin abubuwan da suka faru a harin Boko Haram
Mai Garin Zabarmari Hoto: punchng.com
Asali: UGC

“A cikinsu; matasa masu shekera 13 zuwa 28 har 45 da aka yanka, bakwai daga ciki ne kawai ba a raba kansu da gangar jikinsu ba.” Inji Zanna Lawan Bukar.

“Mun gano gawa 43, daga baya kuma mu ka sake gano wasu 34 da aka kawo aka yi masu sallah. An cigaba da gano wasu gawawwakin a rijiya. Har yanzu ba a gama ganinsu ba.” Mun gano kusan gawawwaki 78.”

“Na san kusan duka wadanda aka kashe. Mafi yawa matasa ne: Gwauraye, sababbin aure da masu iyali kadan."

Ya ce daga cikin wadanda aka hallaka har da wani Tijja da mai dakinsa ta haihu kafin ranar, ya tafi gona domin babu tsabar abinci a gidansa, Allah bai nufa ya dawo da rai ba.

Kun ji cewa ‘Yan Majalisar PDP sun huro wuta, sun ce shugaba Muhammadu Buhari ya cancanci a tunbuke shi daga mulki.

‘Yan Majalisa sun kai ga kiran a tsige shugaban kasar ne saboda matsalar tsaro da ake fama da ita.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng