NHRC: Musa Wapa ya ambaci Ahmad Yariman-Bakura a korafinsa

NHRC: Musa Wapa ya ambaci Ahmad Yariman-Bakura a korafinsa

- NHRC ta kafa wani kwamitin da ke binciken zargin cin wa Musa Wapa zarafi

- Hukumar da ke kula da hakkin Bil Adama ta bukaci ganin Yariman-Bakura

- Tsohon Gwamnan zai bayyana a gaban kwamitin IIP a watan Junairun 2021

Kwamitin bincike mai zaman kansa watau IIP da hukumar NHRC ta kasa ta kafa, ya bukaci Ahmad Sani Yeriman-Bakura ya bayyana gabansa.

Jaridar The Nation ce ta fitar da rahoto a ranar Alhamis, 3 ga watan Disamba, 2020, ta na mai cewa wannan kwamiti yana neman tsohon gwamnan.

Wannan kwamiti ya umarci Sanata Ahmad Sani Yeriman-Bakura ya hallara a ranar 12 ga watan Junairu, 2021, kamar yadda rahoton ya bayyana.

An aika wa tsohon gwamnan na jihar Zamfara wannan sammaci ne bisa zarginsa da ake yi da amfani da jami’an ‘yan sanda wajen cin zarafi.

KU KARANTA: ‘Dan Sanata Adamu Aliero ya auri Dr. Fatima Ahmed Sani Yarima

Wanda ake zargin tsohon Sanatan ya wulakanta ta hannun jami’an tsaro shi ne Alhaji Musa Wapa.

Jaridar ta ce ana zargin fitaccen ‘dan siyasar da tsare Musa Wapa, wanda attajirin ‘dan kasuwa ne, inda aka rika galabaitar da shi bayan an cafke shi.

Alhaji Musa Wapa babban ‘dan kasuwa ne wanda ya samu sabanin kudi har Naira miliyan 23 tsakaninsa da Sanata Ahmad Sani Yeriman-Bakura.

Wanda yake jagorantar wannan kwamitin bincike da hukumar kare hakkin Bil Adama ta Najeriya ta kafa shi ne tsohon Alkali Suleiman Galadima (retd.).

KU KARANTA: An gano a mafarki cewa zan rike kasar nan - Yerima

NHRC: Musa Wapa ya ambaci Ahmad Yariman-Bakura a korafinsa
Ahmad Yariman Bakura Hoto: dabofm.com
Asali: UGC

Suleiman Galadima ya bayyana cewa wanda ya kawo karar ya yawaita ambatar sunan ‘dan siyasar, wanda hakan ya sa aka bukaci ya gabatar da kansa.

A daidai wannan lokaci ne kuma muke jin cewa tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya ce yankin Kudu su fito da Shugaban kasar a 2023.

Tsohon Gwamnan wanda Sanata ne mai wakiltar Kano ta tsakiya a karkashin jam’iyyar APC mai mulki ya sallama wa yankin kudun shugabancin Najeriya.

Ra’ayin babban ‘Dan siyasar na goyon bayan Kudu su karbi mulki ya zo daidai na Nasir El-Rufai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel