Boko Haram: Alaranmomi sun hadu sunyi miliyoyin kafafun addu’o’i a Borno

Boko Haram: Alaranmomi sun hadu sunyi miliyoyin kafafun addu’o’i a Borno

- Jama’a sunyi saukar addu’o’i da Al-kur’ani a dalilin hare-haren ta'addanci

- Mutanen Borno sun taru a wani masallaci sunyi ta aika ruwan du'a’i iri-iri

- Anyi saukar Kur’ani da kuma addu’o’i har fiye da kafa miliyan 40 a zaman

Rahotanni daga BBC Hausa sun bayana cewa an samu wasu mutanen jihar Borno da suka hadu, suka yi addu’o’i domin kawo karshen rikicin Boko Haram.

Wadannan Bayin Allah sun yi addu’o’i fiye da miliyan 41 a jihar Borno domin Allah ya kawo masu maganin ‘yan ta’addan kungiyar nan ta Boko Haram.

BBC ta ce kungiyar Borno Concerned Citizen ta mazauna Borno da suka damu da halin da jihar take ciki ne su ka gudanar da wannan taron addu’o’i a jiya.

A ranar Lahadi, 6 ga watan Disamba, 2020, aka yi wa ‘yan ta’addan ruwan addu’o’i a Maiduguri.

KU KARANTA: Gwamnan Nasarawa, Sule ya ziyarci Jihar Borno

Wata daga cikin ‘yan kungiyar ta masu kishin jihar Borno, Zahra Maiduguri ta shaida wa manema labarai sun yi saukar Kur’ani da addu’o’i 41, 837,016.

Kamar yadda Zahra Maiduguri ta bayyana, Alaranmomi sun ja “Istigifari” 13,669,000 domin tuba ga Allah, sannan sun karanta “Ya Laɗifu’ kafa 10, 688, 000.

Bayan haka, an karanta Suratul Masad kafa miliyan 5, 259, 000 da Ayatul Kursiyy sau 7, 00 da Salatul Fatih kafa 38, 000 da ‘Ya Qahharu’ kafa miliyan guda.

An kuma karanta Suratul Kahf sau shida da wasu lakanoni irinsu Ya Salamu da Bismilla da Salatin Manzon Allah da sauran addu’o’i daga cikin Al-Kur’ani.

KU KARANTA: Sojoji sun ragargaza sansanin 'Yan bindiga a Kaduna

Boko Haram: Alaranmomi sun hadu sunyi miliyoyin kafafun addu’o’i a Borno
Addu’o’in da aka yi a masallacin Goni Modu Hoto: www.bbc.com/hausa
Asali: UGC

Ba a addu’o’i abin ya tsaya ba, wannan gungu da malamai da shugabannin al’umma sun kauda shanu aka zubar da jinanansu domin neman bukata wurin Ubangiji.

Wannan ya zo ne mako guda bayan an kai mugun hari a Zabarmari. Wannan hari ne yayi sanadin mutuwar manoma 43 ko 78 da aka yi wa yankan rago ana ji-ana gani.

Kun ji labarin yadda Boko Haram suka yanka wani Bawan Allah wanda Matar shi ta haihu, ya je neman masu abinci, daga nan bai dawo ba, sai dai aka kawo gawarsa.

Bayan mako guda da harin, Mai Garin Zabarmari ya yi hira da 'yan jarida game da wannan hari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel