Tandja, Amadou Toure, Al Mahdi da Sidi Ould sun mutu a watan Nuwamba

Tandja, Amadou Toure, Al Mahdi da Sidi Ould sun mutu a watan Nuwamba

- Kasashen Afrika sun gamu da rashe-rashe da-dama a ‘yan kwanakin nan

- Sadiq as-Siddiq na Mali ya rasu a yau bayan kamuwa da cutar Coronavirus

- Amadou Touré da Mamadou Tandja da su kayi mulki a baya duk sun rasu

A watan Nuwamban nan an yi rashin shugabanni hudu a Afrika. An fara makoki ne tun a ranar 10 ga watan Nuwamba, har zuwa ranar 26 ga watan mai-ci.

Wanda ya fara mutuwa shi ne Amadou Toumani Touré, daga nan wasu tsofaffin shugabannin kasashen Afrikan suka cigaba da biyo shi har zuwa yau.

Ga jerin tsofaffin shugabannin da aka rasa:

1. Sadiq Al Mahdi

Cutar murar mashako ta Coronavirus ta kashe Sadiq al-Mahdi a ranar 26 ga watan Nuwamba ya na da shekara 82. As-Siddiq ya rike Firayim Minista a dunkulalliyar kasar Sudan har sau biyu.

KU KARANTA: Mutane sun daɗa zuga Donald Trump, ka da ya yarda ya fadi zabe

Marigayin ya yi mulki tsakanin 1966 da 1967, sannan ya sake hawa kujerar daga 1986 zuwa 1989.

2. Tandja Mamamdou

A ranar 24 ga watan Nuwamban nan aka wayi gari da labarin mutuwar tsohon shugaban kasar Nijar, Laftanan Kanal Mamadou Tandja wanda ya yi mulki tsakanin 1999 da 2010.

Mamadou Tandja ya shiga siyasa bayan ya bar gidan soja, amma bai yi nasara ba sai a 1999.

3. Amadou Toumani Toure

A ranar 10 ga watan Nuwamba ne Amadou Toumani Touré ya rasu a wani asibiti a kasar Turkiyya. Amadou Touré ya na kan mulki aka gudanar da zaben farar hula na farko a kasar Mali.

KU KARANTA: Abubuwan alfahari da na kunya da Maradona yayi

Tandja, Amadou Toure, Al Mahdi da Sidi Ould sun mutu a watan Nuwamba
Tandja, Amadou Toure, Al Mahdi da Sidi Ould Hoto: www.lepoint.fr, dsr
Asali: UGC

Bayan nan Marigayin ya rike kasar Mali, shi ne shugaban kasar farar hula na biyu a tarihi.

4. Sidi Ould Cheikh Abdullah

Sidi Mohamed Ould Cheikh Abdallahi, tsohon shugaban kasar Mauritania ya rasu a cikin ‘yan kwanakin nan. Cheikh Abdallahi ya na kan mulki aka hambarar da gwamnati a 2008.

A makon nan ne mu ka samu rahoto cewa ana rade-radin babbar abokiyar takarar Dr. Ngozi Okonjo-Iweala watau Myung-Hee Yo ta hakura da burinta na rike WTO.

'Yar Najeriyar tana kara hangen kanta a WTO musamman bayan ganin Donald Trump ya fadi zabe

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng