Abin alfahari: Adewale Adeyemo mai shekaru 39 zai jagoranci Obama Foundation

Abin alfahari: Adewale Adeyemo mai shekaru 39 zai jagoranci Obama Foundation

- Adewale Adeyemo ya zama Shugaban gidauniyar Barack Obama a Duniya

- Asalin Matashin mai shekara 39 da haihuwa Mutumin kasar Najeriya ne

- Adewale ya yi karatu a Jami’ar California, kuma ya rike mukamai da-dama

Adewale Adeyemo mai shekaru 39 a Duniya ya zama shugaban gidauniyar da tsohon shugaban kasar Amurka, Barack Obama ya kafa watau Obama Foundation.

Gidauniyar Obama Foundation za ta yi kokarin kawo cigaba ne a Duniya inda Adewale Adeyemo ya zama shugaban ta na farko a tarihi bayan kafuwar ta a 2014.

Kafin yanzu Adewale Adeyemo ya kasance mataimakin mai ba gwamnatin Amurka shawara a harkar tattalin arzikin kasashe, ya na cikin matasan da ake ji da su.

Mista Adeyemo rikakken masanin harkar tattalin arziki ne wanda ya yi karatun digiri a fitacciyar jami’ar nan ta Berkley ta birnin Kalifoniya da ke kasar Amurka.

KU KARANTA: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka da zarar an wallafa

Abin alfahari: Adewale Adeyemo mai shekaru 39 zai jagoranci Obama Foundation
Adewale Adeyemo Hoto: Obama Foundation
Asali: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa Adeyemo ya na cikin wadanda su ka taimakawa kasar Amurka wajen fitowa daga cikin matsin tattalin arziki a shekarun baya.

A wannan matsayi, mutumin Najeriyar zai jagoranci wannan gidauniya ta tsohon shugaban Amurkan tare da Martin Nesbitt da babban jami’i David Simas.

Gidauniyar ta na dauke da ma’aikata kusan 200 a halin yanzu wadanda su ke dawainiyar wasu tsare-tsare da za su taimakawa matasa wajen zama manyan gobe.

Bayan ya yi karatu a jami’ar Berkeley, Adewale wanda mutane su ka fi sani da ‘Wally’, ya yi karatun ilmin shari’a a jami’ar nan ta Yale da ke garin Connecticut.

Kamar dai yadda ku ka ji, ba wannan ba ne karon farko da Adewale Adeyemo ya yi aiki da Barack Obama, ya na cikin matasan da su ke gwamnatin Amurka a 2015.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng