Ana zargin Ma’aikatar noma da awon-gaba da N3.08bn zuwa hannun Jami’ai

Ana zargin Ma’aikatar noma da awon-gaba da N3.08bn zuwa hannun Jami’ai

- Wani bincike da Premium Times ta yi ya fallasa danyen aikin Ma’aikatar gona

- An rika dibar kudin Gwamnati ana aika wa asusun wasu Ma’aikatan tarayya

- Tura wa ma’aikaci kudi kai-tsaye irin wannan, ya saba dokar aikin Gwamnati

Jaridar Premium Times ta fitar da wani dogon rahoto na binciken da tayi a game da yadda ma’aikatan harkar gona ta rika aika kudi zuwa asusun wasu tsiraru.

Binciken ya ce tsakanin Satumba zuwa Disamban 2019, an warui Naira biliyan 3.08 daga asusun ma’aikatar gwamnatin tarayya zuwa cikin aljihun wasu ma’aikata 42.

An samu labarin wannan aika-aika da aka yi ne ta manhajar OTP da gwamnatin tarayya ta kawo domin tabbatar da gaskiya wajen aikin ma’aikatun gwamnati a kasar.

Zainab Bala da Mohammed Lawan ne suka fi kowa samun kaso mai tsoka daga cikin wannan kudi; bincike ya nuna an tura masu N255.35m da N246.3 cikin asusun.

KU KARANTA: Kotu ta sa a daure wani 'Dan Majalisa

Ya kamata ace an tura wadannan kudin kwangila ne ga wadanda aka ba aikin ba ma’aikata ba.

A bangaren, Zainab Bala, an aika mata miliyoyin kudi a asusunta ne da sunan za a kafa sashen koyar da aikin gona a sabuwar jami’ar tarayya da ke Zuru, jihar Kebbi.

N100m da N145m suka shiga cikin asusun Aisha Ahmed da Dipnap Nandom Stephen. Bayan nan an tura wa wasu Abdulrahman Ibrahim da Ndakotsu Amina N245m.

Ga jerin ma’aikatan da aka rika aika wa kudi ta asusunsu kai-tsaye, abin da ya saba dokar aiki.

1 ZAINAB BALA 255,350,000

2 MOHAMMED LAWAN 246,298,032

3 NDAKOTSU, MRS. AMINA 174,290,679

4 EBEBI GEORGINA SADIA 172,081,056

5 ABDULRAHMAN, MR. IBRAHIM 171,397,600

6 DIPNAP, MR. NANDOM STEPHEN 145,000,000

7 IJAOBA MUSILIMAT OLAMIDE 140,630,792

8 AJUNWA TOCHUKWU GODWIN 132,114,150

9 AHMED, MR. ARIBO HUSSEIN 126,102,800

10 ONUH OJO SALOME 120,150,201.72

11 ANYAELE, MR. CHARLES OGBONNAYA 107,077,013.85

12 AISHA AHMED 100,000,000

13 MAIMUNA EBILOMA 96,992,000

14 RAUF, MRS. SILIFAT IBIDUNNI 92,985,000

15 ASAAGA BEM 88,299,464.11

16 OKUGO, MRS. STELLA CHINYERE 87,000,000

17 HABIBA SALIHU USMAN 77,337,000

18 EBHOHIMEN, MR. ASEGBE MONDAY 71,466,400

19 NWOKEDI, MRS. PATRICIA EBELE 60,362,000

20 EBENJE, MRS. GLORIA UDOKA 58,614,521

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari tana tunanin sake duba farashin wutar lantarki

Ana zargin Ma’aikatar noma da awon-gaba da N3.08bn zuwa hannun Jami’ai
Ministan harkokin noma Sabo Nanono Hoto: fmic.gov.ng
Source: UGC

21 KUTEYI BOLA ALEX 54,088,706

22 PAM, MR. GABRIEL MARCELLINUS 50,000,000

23 BANJO, MR. SUNDAY JOHN 49,783,200

24 PETER-OKPO, MS. VERA MMAOBONG 46,566,000

25 DAFUNG, MR. YILPRING IBRAHIM 39,393,767

26 ADAMS, MR. . JOSHUA 32,585,943

27 EGWIM, MRS. OZIOMA STELLA 28,715,400

28 JOEL OYETUNJI AKINADE 24,915,979

29 EGBUNU ALADI DORA 24,700,000

30 EDOGBO, MR. SULE 23,534,500

31 UMAR, MR. MOHAMMED SALISU 22,809,000

32 AVIDIME, MS. EWEZE ELIZABETH 21,589,200

33 DIKE AMECHI OTUYA 21,345,614.43

34 IBRAHIM, MR. MOHAMMED 20,626,826.6

35 ADEBIMPE, MRS. OLUWASOLA ESTHER 18,025,159.05

36 ADEBAYO OLORUNTOBI 16,221,750

37 LINUS S E R EYITIMI 14,677,900

38 SULEIMAN, MR. IBRAHIM 14,581,202

39 AKINFOLARIN KUTI, MRS. KATE OLUWATOYIN 10,165,000

40 ONYEDINEFU, MRS. CHIOMA VIRGINIA 9,955,975.78

41 AROKE, MRS. AMORE GRACE 9,109,200

42 ABDULMALIK, MR. WALI SANI 7,900,777.08

Gaba daya dai wadannan ma’aikata sun samu N3, 084, 839, 809.63. Wannan danyen aiki ya ci karo da sashe na 713 na dokar aikin gwamnati a Najeriya.

Kun ji yadda asirin wasu masu yaudarar Jama’a ta yanar gizo domin awon-gaba da kudi ya tonu bayan Interpol da ‘Yan Sanda sunyi nasarar ram da su.

Wadannan hatsabiban ‘Yan Yahoo-Yahoo mutanen Najeriya ne da su ka addabi kamfanoni har da gwamnatocin kasashen ketare da damfara da zamba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel