Adamawa: An dauke wasu mutane 2 daga gidan Shugaban Majalisar dokoki

Adamawa: An dauke wasu mutane 2 daga gidan Shugaban Majalisar dokoki

- An auka gidan Shugaban Majalisar dokokin Adamawa an yi barna a jiya

- ‘Yan Sanda sun tabbatar da cewa an kashe wani Mai gadi 1 da aka samu

- ‘Yan bindigan sun tsere da mutane biyu da aka samu a gidan Iya-Abass

Jaridar Punch ta rahoto cewa wasu ‘yan bindiga da ba a sansu ba sun auka gidan shugaban majalisar dokokin Adamawa, Aminu Iya-Abass, sun yi ta’adi.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun sace wasu mutane biyu daga cikin iyalin Rt. Hon. Aminu Iya-Abass a gidansa da ke Mbamba, a jihar Adamawa.

Kamar yadda jaridar ta fahimta, wadannan miyagu sun auka gidan ‘dan siyasar ne a ranar Alhamis, 5 ga watan Nuwamba, 2020, su ka kashe mutum guda.

KU KARANTA: Sojojin sama sun baza jirage masu luguden bama-bamai

Kara karanta wannan

Ziyarar da Peter Obi Ya Kai wa Dr. Ahmad Gumi ta Jawo Masa Bakin jinin Magoya baya

Jami’an ‘yan sanda sun tabbatar da wannan hari a ranar Juma’a, amma sun karyata rahotannin da ke yawo na cewa an kashe wani ‘dan sanda a harin na jiya,

Majiyar jami’an tsaron ta ce: “A harin, ‘yan bindigan sun kashe wani daga cikin ‘dan banga da ke gadin gidan, yayin da wani jami’in ‘dan sanda ya samu rauni.”

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kakakin ‘yan sanda na jihar Adamawa, Suleiman Nguroje, ya ce ‘yan bindigan sun tsere da wasu mutane.

“A jiya (Alhamis), ‘yan bindiga sun kai hari a wani gida, su ka kashe ‘dan kato-da-gora, kuma su ka tsere da mutum biyu daga gidan.” Inji Suleiman Nguroje.

KU KARANTA: Abin da ya sa aka hana mutanen Najeriya shiga kasar Sin

Adamawa: An dauke wasu mutane 2 daga gidan Shugaban Majalisar dokoki
Aminu Iya Abbas Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Jami’an tsaro sun je gidan da karfe 4:00 na safe, su ka yi kokarin kawo dauki, amma sun makara.

Kara karanta wannan

Abia: ‘Dan Sanda Ya Bindige Abokin Aikinsa Bayan Rikici Ya Hada su

Nguroje ya ce kwamishinan ‘yan sanda na jihar Adamawa, Olugbenga Adeyanju, ya bada umarnin ayi maza a gano wadanda su ka yi wannan mummunan aiki.

A ranar Alhamis, shugaban kasa ya kebe daga shi sai Sarakunan kasar nan. A jiyan, Aso Villa ta karbi bakuncin Tawagar Sarkin Musulmi da Sarakunan Kudu.

Buhari ya zauna da Sultan, Sarkin Kano da wasu Sarakuna, ya nemi su shawo kan matasan kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel