EndSARS: Akwai bukatar Sarakuna su ba gwamnati goyon-baya inji Buhari
- Sarakunan gargajiya su na gana wa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari
- Sultan Alhaji Abubakar Sa’ad III da Ooni da Ife su na cikin wannan tawagar
- Haka zalika Sarakunan Kano, Nufe da yankin Twon-Brass sun samu halarta
A ranar Alhamis, 5 ga watan Nuwamba, 2020, jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa shugaba Muhammadu Buhari ya zauna da manyan sarakuna.
A taron da aka yi tsakanin Muhammadu Buhari da sarakunan gargajiya a ranar Alhamis din an tabo bukatun da su ke damun matasan Najeriya a yau.
Shugaban kasar ya jaddada bukatar samun goyon bayan sarakuna wajen tafiyar da gwamnatinsa.
Buhari ya ce: “Domin mu yi nasara a duka wannan, mu na bukatar gudumuwarku wajen aika sakonmu. Kusancinku da mutanen ya ba ku daman a musamman na yin tasiri.”
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya sa labule da Sarakunan gargajiya (Hotuna)
Shugaba Buhari ya bayyana sarakunan da masu adana al’adun al’umma, har ya yi kira gare su da su zama masu adalci, ka da su nuna son rai wajen aikinsu.
Femi Adesina ya rahoto shugaban kasar ya na cewa: “Babu inda za a buya game da yadda za a shawo kan matsalar tsaro, rashin aikin yin matasa, da samar da aiki.
Shugaban kasar ya shiga taro ne da sarakunan gargajiyan ne daga duka bangarorin kasar nan. Rahotanni sun ce an shiga wannan taro ne da rana a Aso Villa.
Sarakunan da su ka yi magana a madadin takwarorinsu a wannan zama su su ne: Sarkin Musulmi, Abubakar Sa’ad da Ooni na kasar Ife, Adeyeye Ogunwusi.
KU KARANTA: Dangote ya ci karfin aikin matatar danyen man da ya ke ginawa
Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya na cikin wannan babbar tawaga.
Sarakunan duk su na dauke da takunkumin rufe fuska kamar yadda hukumomin lafiya su ka gindaya sharudan yaki da cutar murar nan ta COVID-19.
Hukumar dillancin labarai na kasa ta dauki hoton shigar manyan kasar zuwa fadar shugaban Najeriya na Aso Villa da ke babban birnin tarayya Abuja.
A cikin hoton za a iya ganin Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar a gaba yayin da Mai martaba Aminu Ado Bayero da su Shehun Borno su ke bayansa.
KU KARANTA: Babu shakka, mun gaza - Ministar kudi
Shi ma Amanyanabo na kasar Twon-Brass, Mai martaba Alfred Diete-Spiff da wasu Sarakunan yankin Neja-Delta duk sun samu damar ganin shugaban kasar.
Kawo yanzu ba mu da labarin wainar da manyan kasar su ke toya wa da shugaban Najeriyar.
Ministar ta ce idan ana so kasar nan ta cigaba, dole a rika dama wa da Matasa masu jini a jika
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng