Zamfara: Rundunar soji ta baza boyayyun jiragen zamani masu leken asiri da ruwan wuta

Zamfara: Rundunar soji ta baza boyayyun jiragen zamani masu leken asiri da ruwan wuta

- NAF ta sanar da cewa za ta baza jiragen yaki na zamani guda hudu zuwa jihar Zamfara

- A cewar Saddique Abubakar, babban hafsan rundunar sojojin sama, jirage za su yi aiki a sauran jihohin arewa maso yamma

- Saddique ya kara da cewa yanzu haka Najeriya na jiran isowar wasu sabbin jiragen yaki 17 daga kasar Amurka

Rundunar sojin saman Nigeria (NAF) ta ce zata tura da jiragen sama marasa matuki zuwa jihar Zamfara don bunkasa aikinta na yaki da 'yan bindiga a jihar.

Shugaban rundunar sojojin sama, Air Marshal Saddique Abubakar, ne ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyara jihar zamfara a ranar Alhamis.

Saddique ya ce Najeriya za ta tura irin wadannan jirage na musamman guda hudu yayin da NAF ke jiran isowar wasu sabbin jiragen yaki guda 17.

A cewar Saddique, ya kai ziyara jihar ne don kara samun bayanai da duba matakin gwamnatin tarayya na tura karin kayyayaki don kara tallafawa aikin yaki da 'yan ta'addar da suka addabi jihar.

Ya ce muhimmacin ziyarar da kuma samar da kayan aiki na zamani shine domin bunkasa aiyukan sama ba a iya Zamfara kawai ba, har ma da yankin arewa maso yammacin gaba daya.

Zamfara: Rundunar soji ta baza boyayyun jiragen zamani masu leken asiri da ruwan wuta
Saddique ABubakar da dakarun NAF
Asali: Facebook

"Mu na tsammanin jiragen yaki na zamani samfurin UAV guda hudu da za su yi aiki daga Gusau har zuwa ko ina a Zamfara, Katsina, Sokoto, Kebbi, da jihar Kaduna.

"Bayan jihar Zamfara, jiragen marasa matuki za su yi aiki a jihar Gombe da jihar Borno.

"Mun zo nan ne domin neman goyon bayan gwamnatin jiha da tabbatar da an gudanar da aikin cikin tasiri", a cewar Saddique.

Sannan ya cigaba da cewa; "nan bada dadewa ba zamu kaddamar da ginin titin jirgin sama don jiragen su yi aiki a nan Zamfara.

DUBA WANNAN: Karya kake, ba'a sulhunta rikicin APC a Zamfara ba - Marafa ya bukaci Buni ya yi murabus

"Mu na neman fili daga gwamnatin jiha don samun karin wurare da masauki na jami'anmu da aka tura jihar.

"A yanzu haka mu na tsammanin jiragen yaki 17 wanda 12 daga ciki zasu zo ne daga kasar Amurka.

"Kun san jami'anmu da dakaru sun dade a Amurka don karbar horo. Yanzu haka akwai jami'ai 195 a kasashe tara na duniya don horo daban-daban da kuma kula da jiragenmu".

Saddique ya yaba da goyon baya da hadin kai da NAF ke samu daga masarautun gargajiya da malaman addinai da kuma sauran jama'a.

A nasa bangaren, gwamna Matawalle ya yabawa shugaba Buhari a kan goyon bayan da yake bawa jihar Zamfara domin yakar rashin tsaro.

KARANTA: Magidanci ya yi garkuwa da diyarsa a Kano, ya bukaci matarsa ta biya N2m kudin fansa

Matawalle ya ce "kamar yadda muka sani, a satin da ya gabata na je Abuja, inda na nemi agajin gaggawa daga shugaban kasa a kan matsalar rashin tsaro.

"Muna godiya ga gwamnatin tarayya da ta bamu agajin gaggawa ga matsalar tsaro da ta addabi jihar Zamfara. Wannan ziyara ta babban hafsan sojojin sama tana daya daga cikin ribar ziyarata zuwa Abuja.

"Matsalar tsaro ba akan jami'an tsaro kawai take ba, dan haka ina kira ga jama'ar mu su cigaba da bada goyan bayansu ga sojojin Nigeria da sauran hukumomin tsaro don ganin an yi nasara wajen aikin."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel